Musulunci
baya

44. Ad-Dukhaan

1Ḥ. M̃

2Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani

3Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi

4A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne

5Umurni na daga wurin Mu. Lalle Mũ ne Muka kasance Mãsu aikãwã

6Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani

7(Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka)

8Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko

9A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka

10Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne

11Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi

12Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne

13Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)

14Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa* ne, mahaukaci

15Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin)

16Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne

17Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu

18(Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku

19Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne

20Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni

21Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni

22Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi

23(Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku)

24Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa

25Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari

26Da shuke-shuke da matsayi mai kyau

27Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu

28Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam

29Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka *a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba

30Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa

31Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna

32Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne

33Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna

34Lalle waɗannan mutãne*, haƙĩka, sunã cẽwa

35Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba

36Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya

37shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi

38Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã

39Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba

40Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya

41Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba

42fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai

43Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã)

44Ita ce abincin mai laifi

45Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna

46Kamar tafasar ruwan zãfi

47(A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm

48Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi

49(A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma

50Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi

51Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce

52A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari

53Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna

54Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyawun idãnu, mãsu girmansu

55Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro)

56Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm

57Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma

58Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa

59Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath