Musulunci
baya

38. Sa'ad

1Ṣ̃, Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni mai hukunce-hukunce

2Ã'a, waɗanda suka kãfirta sunã cikin girman kai (ga rikon al'ãdunsu) da sãɓãni (tsakãnin jũnansu)

3Da yawa Muka halakar da wani ƙarni, a gabãninsu, suka yi kira (nẽman cẽto), bãbu lõkacin kuɓucewa

4Kuma suka yi mãmãki dõmin Mai gargaɗi, daga cikinsu, ya je musu. Kuma kãfirai sukace, "Wannan mai sihiri ne, maƙaryaci

5Shin, yã sanya gumãka duka su zama abin bautawa guda? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmaki

6Shũgabanni daga cikinsu, suka tafi (suka ce),"Ku yi tafiyarku, ku yi haƙuri a kan abũbuwan bautawarku. Lalle wannan, haƙiƙa, wani abu ne ake nufi

7Ba mu taɓa ji ba, game da wannan a cikin addinin ƙarshe. Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya

8Shin, an saukar da Alƙur'ãni ne a kansa, a tsakãninmu (mũ kuma ba mu gani ba)?" Ã'a, su dai sunã cikin shakka daga hukunciNa Ã'a, ba su i da ɗanɗanar azãba ba

9Ko kuma a wurinsu ne ake ajiye taskõkin rahamar Ubangijinka, Mabuwãyi, Mai yawan kyauta

10Kõ kuma sũ ne da mallakar sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu? To sai su hau a cikin sammai (dõmin, su hana saukar Alƙur'ãni ga Muhammadu)

11Rundunõni ne abin da ke can, rusassu, na ƙungiyõyinsu

12Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, da Ãdãwa da Fir'auna mai turãkun (da suka kafe mulkinsa)

13Da Samũdãwa da mutãnen Luɗu da ma'abũta ƙunci, *waɗancan ne ƙungiyõyin

14Bãbu kõwa a cikinsu fãce ya ƙaryata Manzanni, sabõda haka azãbãTa ta wajaba

15Kuma waɗannan *bã su jiran kõme fãce tsãwã guda, wadda bã ta da hani

16Kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka gaggauta mana da rabonmu, a gabãnin rãnar bincike

17Ka yi haƙuri bisa ga abin da suke faɗa (na izgili), kuma ka ambaci bãwan Mu Dãwũda ma'abũcin ƙarfin ibãda. Lalle, shi, mai mayar da al'amari ga Allah ne

18Lalle Mũ, Mun hõre duwãtsu tãre da shi, sunã yin tasbĩhi maraice da fitõwar rãnã

19Da tsuntsãye waɗanda ake tattarawa, kõwannensu mai kõmãwa ne a gare shi

20Kuma Muka ƙarfafa mulkinsa, kuma Muka bã shi hikima* da rarrabẽwar magana

21Kuma shin, lãbãrin mãsu husũma ya zo maka, a lõkacin da suka haura gãrun masallaci

22A lõkacin da suka shiga ga Dãwũda, sai ya firgita daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro, masu husuma biyu ne; sãshenmu ya zãlunci sãshe. Sabõda haka, ka yi hakunci a tsakãninmu da gaskiya. Kada ka ƙẽtare haddi kuma ka shiryar da mu zuwa, ga tsakar hanya

23Lalle wannan dan'uwãna ne, yanã da tunkiya casa'in da tara, kuma inã da tunkiya guda, sai ya ce: 'Ka lãmunce mini ita. Kuma ya buwãye ni ga magana

24(Dãwũda) ya ce: "Lalle, haƙiƙa ya zãlunce* ka game da tambayar tunkiyarka zuwa ga tumakinsa. Kuma lalle ne mãsu yawa daga abõkan tarayya, haƙiƙa, sãshensu na zambatar sãshe fãce waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai." Kuma Dãwũda ya tabbata cẽwa Mun fitine shi ne, sabõda haka, ya nẽmi Ubangijinsa gãfara, kuma ya fãɗi yanã mai sujada, kuma ya mayar da al'amari ga Allah

25Sabõda haka Muka gãfarta masa wancan, kuma lalle yanã da wata kusantar daraja a wurin Mu, da kyaun makõma

26Yã Dãwũda! Lalle Mũ Mun sanya ka Halĩfa a cikin ƙasã. To, ka yi hukunci tsakãnin mutãne da gaskiya, kuma kada ka biye wa son zũciyar, har ya ɓatar dakai daga hanyar Allah. Lalle waɗanda ke ɓacẽwa daga hanyar Allah sunã da wata azãba mai tsanani dõmin abin da suka manta, a rãnar hisãbi

27Kuma ba Mu halitta sama da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu ba a kan ƙarya. Wannan shĩ ne zaton waɗanda suka kãfirta. To, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga wutã

28Kõ zã Mu sanya waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai kamar waɗanda suke mãsu barna ne a cikin ƙasa? Ko kuma za Mu sanya masu bin Allah da taƙawa kamar fãjirai makarkata

29(Wannan) Littãfi ne, Mun saukar da shi zuwa gare ka, yanã, mai albarka, dõmin su lũra da ãyõyinsa, kuma don mãsu hankali su riƙa yin tunãni

30Kuma Muka bai wa Dãwũda Sulaimãn. Mãdalla da bãwanMu, shi. Lalle shi (Sulaimãn) mai mayar da al'amari ne ga Allah

31A lõkacin da aka gitta masa dawãki mãsu asali, *a lõkacin maraice

32Sai ya ce: "Lalle nĩ, na fĩfĩta son dũkiya daga tunãwar Ubangijina, har (rãnã) ta faku da shãmaki

33Ku mayar da su a gare ni." Sai ya shiga yankansu* da takõbi ga ƙwabrukansu da wuyõyinsu

34Kuma lalle haƙĩƙa, Mun fitini* Sulaiman kuma Muka jẽfa wani jikin mutum a kan karagarsa. Sa'an nan ya mayar da al'amari zuwa gare Mu

35Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka gãfarta mini, kuma Ka bã ni mulki wanda bã ya kamãta da kõwa daga bãyãna.* Lalle Kai, Kai ne Mai yawan kyauta

36Sabõda haka Muka hõre masa iska* tanã gudu da umurninsa, tãna tãshi da sauƙi, inda ya nufa

37Da shaiɗanu dukan mai gini, da mai nutsa (a cikin kõguna)

38Waɗansu, ɗaɗɗaure a cikin marũruwa

39Wannan kyautar Mu ce. Sai ka yi kyauta ga wanda kake so, ko kuma ka riƙe, bãbu wani bincike

40Kuma lalle, haƙĩƙa yanã da kusantar daraja a wurin Mu da kyaun makõma

41Kuma ka ambaci bãwan Mu Ayyũba* a lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, ya ce: "Lalle nĩ, Shaiɗan yã shãfe ni da wahala da kuma wata azãba

42Ka shura da ƙafarka. Wannan abin wanka ne mai sanyi da abin shã

43Kuma Muka bã shi iyalansa da kwatankwacinsu tãre da su sabõda rahama daga gare Mu, da tunãtarwa ga mãsu hankali

44Kuma ka riƙi wata ƙulla da hannunka, ka yi dũka da ita kuma kada ka karya rantsuwarka. Lalle Mũ, Mun sãme shi mai haƙuri. Madalla da bãwa, shĩ Lalle shĩ mai mayar da al'amari ga Allah ne

45Kuma ka ambaci bãyin Mu: Ibrahĩm da ls'hãƙa da Ya'aƙũba, ma'abũta ƙarfin (ɗaukar umurnin Mu) da basĩra

46Lalle Mũ, Mun keɓance su game da wata, tsattsarkar aba: Hukunce-hukuncen gidan dũniya (mai tunãtar da su Lãhira)

47Kuma lalle sũ a wurin Mu, tabbas, sunã daga zãɓaɓɓu, mafĩfĩta

48Kuma ka ambaci Isma'ĩla da llyãs da Zulkifli, kuma dukansu sunã daga zãɓaɓɓu

49Wannan tunãtarwa ce, kuma lalle mãsu bin Allah da taƙawa, sunã da kyakkyawar makõma

50Gidãjen Aljannar zama, alhãli kuwa tanã abar buɗe wa kõfõfi sabõda su

51Sunã gingincire a cikinsu, sunã kira a cikinsu, ga 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, da abin shã

52Kuma a wurinsu akwai mãtan aure mãsu gajarta ganinsu ga mazansu, tsãrar jũna

53Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi ga rãnar hisãbi

54Lalle wannan, haƙĩƙa, azurtarwar Mu ce, bã ta ƙãrẽwa

55Wannan shĩ ne kuma lalle makangara, haƙĩƙa, sunã da mafi sharrin makõma

56Jahannama, sunã shigarta. To, shimfiɗar tã mũnana, ita

57Wannan shĩ ne! To, su ɗanɗane shi: ruwan zãfi ne da ruɓaɓɓen jini

58Da wani daga siffarsa nau'i-nau'i

59Wannan wani yanki ne mai kũtsawa tãre da ku, bãbu marãba a gare su, lalle sũ, mãsu shiga Wutã ne

60Suka ce: "Ã'a, ku ne bãbu marãba a gare ku, kũ ne kuka gabãtar da shi a gare mu." To, matabbatar tã mũnana (ita wutar)

61Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Wanda ya gabãtar da wannan a gare mu, to, Ka ƙãra masa azãba, ninki, a cikin wutã

62Kuma suka ce: "Mẽ ya sãme mu, bã mu ganin waɗansu mazãje, mun kasance munã ƙidãya su daga asharãrai

63Shin, mun riƙe su abin izgili ne kõ idãnunmu sun karkata daga gare su ne

64Lalle wannan, haƙĩƙa, gaskiya ne, husũmar mutãnen wutã

65Ka ce: "Nĩ mai gargaɗikawai ne, kuma babu wani abin bautawa sai Allah, Makaɗaici, Mai tilastawa

66Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu Mabuwãyi, Mai gãfara

67Ka ce: "Shĩ (Alkur'ãni) babban lãbãri ne mai girma

68Kũ, mãsu bijirẽwa ne daga gare shi

69Wani ilmi bai kasance a gare ni ba game da jama'a (malã'iku) mafi ɗaukaka a lõkacin da suke yin husũma

70Ba a yi mini wahayin kõme ba face cẽwa ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanãwa

71A lõkacin da Ubangijinka Ya ce wa malã'iku, "Lalle Nĩ Mai halitta mutum ne daga lãkã

72Sa'an nan idan Nã daidaita shi, kuma Na hũra (wani abu) daga Ruhĩ Na a cikinsa to ku fãɗi kunã mãsu sujada a gare; shi

73Sai malã'ikun suka yi sujada dukansu, gabã ɗaya

74Fãce Iblis, ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai

75(Allah) Ya ce, "Yã Ibilis! Mẽ ya hana ka, ka yi sujada ga abin da Nã halitta da HannayeNa biyu? Shin, kã yi girman kai ne, kõ kuwa kã kasance daga maɗaukaka ne

76Ya ce, "Nĩ, mafifici ne daga gare shi: Kã halitta ni daga wutã, kuma Kã halitta shi daga lãkã

77Ya ce, "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai la'ananne ne

78Kuma lalle a kanka akwai la'anaTa har zuwa rãnar sakamako

79Ya ce, "Ya Ubangijina! To, Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar da su

80Ya ce, "To, lalle kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri

81Zuwa ga yinin lõkaci sananne

82Ya ce, "To, inã rantsuwa da buwãyar Ka, lalle, inã ɓatar da su gabã ɗaya

83Fãce bãyin Ka tsarkakakku daga gare su

84(Allah) Ya ce, "To, (wannan magana ita ce) gaskiya. Kuma gaskiya Nake faɗa

85Lalle zã Ni cika Jahannama daga gare ka, kuma daga wanda ya bĩ ka daga gare su, gabã ɗaya

86Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra, a kansa kuma bã ni daga mãsu ƙãƙalen faɗarsa

87Shĩ (Alkur'ãn) bai zama ba fãce ambato ne ga dukan halitta

88Kuma lalle zã ku san babban lãbãrinsa* a bayan ɗan lõkaci

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath