Musulunci
baya

20. Ta-Ha

1T,H

2Ba Mu saukar da Alƙur'ãni a gare ka dõmin ka wahala ba

3Fãce dõmin tunãtarwa ga wanda ke tsõron Allah

4(An saukar da shi) saukarwa daga wanda Ya halitta ƙasa da sammai maɗaukaka

5Mai rahama, Ya daidaita* a kan Al'arshi

6Abin da yake a cikin sammai nãsa ne, da abin da yake a cikin ƙasa da abin da yake a tsakãninsu da abin da ke ƙarƙashin turɓãya

7Kuma idan ka bayyana da magana, to, lalle Shi, Yanã sanin asĩri da mafi bõyuwa

8Allah bãbu abin bautãwa fãce Shi. Yanã da sunãye mafiya kyau

9Kuma shin, lãbarin Mũsã yãje maka

10A lõkacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyãlinsa, "Ku dãkata. Lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wuta tsammãnĩna in zo mukuda makãmashi daga gare ta, kõ kuwa in sãmi wata shiriya a kan wutar

11Sa'an nan a lõkacin da ya je mata, aka kira shi, "Ya Mũsã

12Lalle ne, Nĩ ne Ubangijnka, sai ka ɗẽbe takalmanka* Lalle ne kanã a rãfin nan abin tsarkakẽwa, ¦uwa

13Kuma Nĩ nã zãɓe ka. Sai ka saurãra ga abin da ake yin wahayi

14Lalle, Nĩ Ni ne Allah. Bãbu abin bautawa fãce Ni. Sai ka bauta Mini, kuma ka tsayar da salla dõmin tuna Ni

15Lalle ne Sa'a mai zuwa ce, lnã kusa da In ɓõye ta dõmin a sãka wa dukan rai da abin da yake aikatãwa

16Sabõda haka, kada wanda bã ya yin ĩmãni da ita kumaya bi son zuciyarsa, ya taushe ka daga gare ta har ka halaka

17Kuma wãce ce waccan ga dãmanka yã Mũsa

18Ya ce: "Ita sandãta ce, inã dõgara a kanta, kuma inã kakkaɓar ganye da ita a kan ƙananan bisãshẽna kuma inã da waɗansu bukãtõci* na dabam a gare ta

19Ya ce: "Ka yi jĩfa da ĩta, yã Mũsã

20Sai ya jẽfa ta. Sai gã ta dabbar macĩjiya, tanã tafiya da gaggãwa

21Ya ce: "Ka kãma ta kuma kada ka ji tsõro. Za Mu mayar da ita ga hãlinta na farko

22Kuma ka haɗa hannunka zuwa ga damtsenka, ya fita yanã fari, bãbu sõfane, wata ãyã ta dabam

23Dõmin Mu nũna maka daga ãyõyin Mu manya

24Ka tafi zuwa ga Fĩr'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (da girman kai)

25Ya ce: "Ya Ubangiji! Ka buɗa* mini, ƙirjĩna

26kuma ka sawwake mun Al'amari na

27Kuma Ka warware mini wani ƙulli daga harshẽna

28Su fahimci maganãta

29Kuma Ka sanya mini wani mataimaki daga mutãnena

30Hãrũna ɗan uwana

31Ka ƙarfafa halittata da shi

32Kuma Ka shigar da shi a cikin al'amarina

33Dõmin mu tsarkake Ka da yawa

34Kuma mu tuna Ka da yawa

35Lalle Kai, Ka kasance Mai gani gare mu

36Ya ce: "Lalle ne, an bã ka rõƙonka, yã Mũsã

37Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun yi wata baiwa gare ka a wani lõkacin na dabam

38A lõkacin da Muka yi wahayin abin da aka yi wahayi zuwa ga uwarka

39Cẽwa, Ki jẽfa shi a cikin akwatin nan, sa'an nan ki jẽfa shi a cikin kõgi, sa'an nan kogin ya jefa shi a gãɓa, wani maƙiyi Nãwa kuma maƙiyi nãsa ya ɗauke shi.' Kuma Na jẽfa wani so daga gare Ni a kanka. Kuma dõmin a riƙe ka da kyau a kan gan iNa

40A sa'ad da 'yar'uwrka ke tafiya har ta ce, shin, in shiryar da ku ga wanda ke rẽnonsa?' Sai Muka mayar da kai zuwa ga uwarka dõmin idonta ya yi sanyi* kuma bã zã ta yi baƙin ciki ba. Kuma kã kashe wani rai, sa'an nan Muka tsẽrar da kai daga baƙin ciki, kuma Muka fitine ka da waɗansu fitinõni. Sa'an nan ka zauna shẽkaru a cikin mutãnen Madyana. Sa'an nan kuma ka zo a kan wata ƙaddara, yã Mũsã

41Kuma Na zãɓe ka dõmin Kaina

42Ka tafi kai da ɗan uwanka game da ãyõyi Na, kuma kada ku yi rauni ga ambatõ Na

43Ku tafi kũ biyu zuwa ga Fir'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (ga girman kai)

44Sai ku gaya masa magana mai laushi,* tsammãninsa yanã tunãwa kõ kuwa ya ji tsõro

45Su biyu suka ce: "Ya Ubangijinmu! Lalle ne munã tsõron ya yi gaggawa a kanmu, kõ ya ƙẽtare haddi

46Ya ce: "Kada ku ji tsõro. Lalle Nĩ, Inã tãre da ku, Inaji, kuma Inã gani

47Sai ku jẽ masa sa'an nan ku ce, Lalle mũ, Manzanni biyune na Ubangijinka, sai ka saki Banĩ Isrã'ĩla tãre da mu. Kuma kada ka yi musu azãba. Haƙĩƙa mun zomaka da wata ãyã daga, Ubangijinka. Kuma aminci ya tabbata ga wanda ya bi shiriya

48Lalle mũ, haƙĩƙa, an yi wahayi zuwa gare mu, cẽwa azãba tanã a kan wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya

49Ya ce: "To, wãne ne Ubangijinku? Ya Mũsã

50Ya ce: "Ubangijin mu Shi ne wanda Ya bai wa dukan kõme halittarsa, sa'an nan Ya shiryar

51Ya ce: "To, mẽne hãlin ƙarnõnin farko

52Ya ce: "Saninsu yanã a wurin Ubangijĩna, Ubangijĩna bã Ya ɓacẽwa kuma bã Ya mantuwa

53Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma Ya shigar muku da hanyõyi a cikinta, kuma Ya saukar da ruwa daga sama." Sa'an nan game da shi* Muka fitar da nau'i-nau'i daga tsirũruwa dabam-dabam

54Ku ci kuma ku yi kiwon dabbõbin ni'imarku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyõyi ga masu hankali

55Daga gare ta* Muka halitta ku, kuma a cikinta Muke mayar da ku, kuma daga gare ta Muke fitar da ku a wani lõkaci na dabam

56Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun nũna masa ãyõyin Mu dukansu sai ya ƙaryata, kuma ya ƙiya

57Ya ce: "Shin kã zo mana ne dõmin ka fitar da mu daga ƙasarmu game da sihirinka, yã Mũsã

58To, lalle ne munã zo maka da wani sihiri irinsa. Sai ka sanya wani wa'adi a tsakãninmu da tsakãninka bã mu sãɓa masa mũ kai kuma, bã ka sãɓãwa, a wani wuri mai dãcẽwa

59Ya ce: "Wa'adinku shi ne rãnar ƙawa kuma a tãra mutãne da hantsi

60Sai Fir'auna ya jũya, sa'an nan ya tãra mugunyar dabãrarsa, sa'an nan kuma ya zo

61Mũsã ya ce musu, "Kaitõnku! Kada ku ƙirƙira ƙarya ga Allah har Ya tumɓuke ku da wata azãba. Kuma wanda ya ƙirƙira ƙarya, yã tãɓe

62Sai suka yi jãyayya ga al'amarinsu a tsakãnin su kuma suka asirta gãnawa

63Suka ce: "Lalle ne waɗannan biyun, haƙĩƙa masihirta ne sunã nufin su fitar da ku daga ƙasarku* game da sihirinsu kuma su tafi da tabĩ'arku mafĩficiya

64Sai ku haɗa dabãrarku sa'an nan kuma ku tafi a sahu guda, kuma haƙĩƙa, wanda ya rinjãya, a yau, ya rabbanta

65Suka ce: "Ya Mũsã! Imma ka jefa, ko kuma mu kasance farkon mai jẽfawa

66Ya ce: "Ã'a, ku jẽfa." Sai gã igiyoyinsu da sandunansu anã sũranta su a gare shi, daga sihirinsu, lalle sunã tafiya da sauri

67Sai Mũsã ya ji tsõro a cikin ransa

68Muka ce: "Kada ka ji tsõro. lalle kai ne mafi ɗaukaka

69Kuma ka jẽfa abin da ke a cikin hannun dãmanka, ta cafe abin da suka aikata. Lalle ne abin da suka aikata mãkircin masihirci ne kuma masihirci bã ya cin nasara a duk inda ya je

70Sai aka jẽfar da masihirtan sunã mãsu sujada, suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin Hãrũna da Mũsã

71Ya ce: "Kun yi ĩmãni sabõda shi a gabãnin in yi muku izni? Lalle shĩ, haƙĩƙa, babbanku ne wanda ya sanar da ku sihirin! To, lalle ne zan kakkãtse hannayenku da ƙafãfunku a tarnaƙi kuma lalle zan tsĩre ku a cikin kututturan itãcen dabĩno, kuma lalle zã ku sani wanenmu ne mafi tsananin azãba kuma wãne ne mafi wanzuwar (azãba)

72Suka ce: "Bã zã mu fĩfĩta ka ba faufau a kan abin da ya zo mana na hujjõji. Munã rantsuwa da wanda Ya ƙãga halittarmu sai ka hukunta abin da kake mai hukuntãwa, ai kanã ƙãre wannan rãyuwar dũniya kawai ne

73Lalle mũ, mun yi ĩmãni da Ubangijinmu dõmin Ya gãfarta mana laifuffukanmu da abin da ka tĩlasta mu a kansa na sihiri. Kuma Allah ne Mafi alhẽri, kuma Mafi wanzuwa

74Lalle* shĩ wanda ya je wa Ubangijinsa yanã mai laifi, to lalle ne yanã da Jahannama, bã ya mutuwa a cikinta kuma bã ya rãyuwa

75Kuma wanda ya je Masa yanã mai ĩmãni, alhãli kuwaya aikata aikin ƙwarai to waɗannan sunã da darajõji maɗaukaka

76Gidãjen Aljannar zama kõguna na gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu. Kuma wannan ne sakamakon wanda ya tsarkaku

77Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa, "Ka yi tafiyar dare da bãyiNa. Sa'an nan ka dõka musu hanya a cikin tẽku tana ƙẽƙasasshiya, bã ka tsõron riska, kuma bã ka fargabar nutsẽwa

78Sai Fir'auna ya bi su game da rundunarsa. Sai abin da ya rufe su daga tẽku ya rufe su

79Kuma Fir'auna ya ɓatar da mutãnensa, kuma bai shiryar (dasu) ba

80Yã Banĩ Isrã'ĩla! Lalle Mun tsẽrar da ku daga maƙiyinku, kuma mun yi muku wa'adi a gẽfen Dũtsen nan na dãma, kuma Mun sassaukar da darɓa da tattabaru dõminku

81Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurtã ku kuma kada ku ƙẽtare haddi a cikinsa har fushĩ Na ya sauka a kanku. Kuma wanda fushĩ Na ya sauka a kansa, to, lalle ne, ya fãɗi

82Kuma lalle Nĩ haƙĩƙa Mai gãfara ne ga wanda ya tũba kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, sa'an nan kuma ya nẽmi shiryuwa

83Kuma mẽne ne ya gaggautar* da kai ga barin mutãnenka? Yã Mũsã

84Ya ce: "Su ne waɗannan a kan sãwũna, kuma na yi gaggãwa zuwa gare Ka, yã Ubangiji! Dõmin Ka yarda

85Ya ce: "To, lalle ne, haƙĩƙa, Mun fitini, mutãnenka daga bayãnka, kuma sãmiri ya ɓatar da su

86Sai Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa yanã mai hushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Yã mutãnẽna! shin, Ubangijinku bai yi muku wa'adi ba, wa'adi mai kyau? Shin, lõkacin ya yi tsãwo a kanku ne, kõ kun yi nufi ne wani hushi ya sauka a kanku daga Ubangijinku, sabõda haka kuka sãɓã wa alkawarĩna

87Suka ce: "Ba mu sãɓa wa alkawarinka* ba da ĩkonmu kuma amma an ɗõra mana waɗansu kãya masu nauyi daga abin ƙawar mutãnen ne, sai muka jẽfar da su. Sa'an nan kamar haka ne sãmiri ya jẽfa

88Sai ya fitar musu da wani maraƙi, jikin mutãne, yanã rũri, sa'an nan suka ce: wannan ne gunkinku kuma gunkin Mũsã, sai ya manta

89Shin, to, bã su ganin cẽwabã ya mayar musu da magana, kuma bã ya mallakar wata cũta a gare su, kuma bã ya mallakar amfãni

90Kuma, haƙĩƙa, Hãrũna yã ce musu daga gabãni, "Yã mutãnẽna! Lalle an fitinẽ ku da shi ne kawai. Kuma lalle Ubangijinku Mai rahama ne, sai ku bi ni, kuma ku yi ɗã'ã ga umarnĩna

91Suka ce ba zamu gushe ba muna bauta a gareshi ba har sai Musa dawo

92(Mũsã) ya ce: "Yã Hãrũna! Mẽ ya hane ka, sa'ad da kagan su sun ɓace

93Ba ka bĩ ni ba! Shin, to, ka sãɓã wa umarnina ne

94(Hãrũna) ya ce: "Yã ɗãn'uwãna! Kada ka yi kãmu ga gẽmũna kõ ga kaina. Lalle nĩ, nã ji tsõron ka ce: Ka rarraba a tsakãnin Banĩ Isrã'ĩla kuma ba ka tsare maganata ba

95(Mũsã) ya ce: "Mẽne ne babban al'amarinka? Kai Sãmiri

96(Sãmiri) ya ce: "Nã ga abin da ba su gan shi ba shi, sai na yi damƙa, damƙa guda daga kufan sãwun Manzon, sa'an nan na jẽfa ta. Kuma haka dai raina ya ƙawãta mini

97(Mũsã) ya ce: "To, ka tafi, sabõda haka lalle ne kanã da a cikin rãyuwarka, ka ce 'Bãbu shãfa' kuma kanã da wani ma'alkawarta, bã zã a sãɓa maka gare ta ba. Kuma ka dũba zuwa ga gunkinka wanda ka yini a kansa kanã mai lazimta. Lalle ne muna ƙõne shi,* sa'an nan kuma munã shẽƙe shi, a cikin tẽku, shẽƙẽwa

98Abin sani kawai abin bautãwarku Allah kawai ne wanda bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi kuma Yã yalwaci* dukkan kõme da ilmi

99Kamar wancan ne Muke lãbartãwa* a gare ka, daga lãbãran abin da ya gabãta, alhãli kuwa haƙĩƙa, Mun bã ka zikiri (Alƙur'ãni) daga gun Mu

100Wanda ya kau da kai daga gare shi, to, lalle shĩ, yanã ɗaukar wani nauyi a Rãnar ¡iyãma

101Sunã madawwama a cikinsa, kuma yã mũnana ya zama abin ɗauka, a Rãnar ¡iyãma

102A Rãnar da ake hũrãwa a cikin ƙãho kuma Munã tãra mãsu laifi, a rãnar nan, sunã mãsu shũɗãyen idãnu

103Suna ɓõye magana a tsakãninsu, (Sunã ce wa jũna) "Ba ku zauna ba (a cikin dũniya) fãce kwãna gõma

104Mu ne mafi sani ga abin da suke faɗa a sa'ad da mafĩficinsu ga hanya ke cẽwa, "Ba ku zauna ba fãce a yini guda

105Kuma sunã tambayar ka daga duwãtsu* sai ka ce: "Ubangijina Yana shẽƙe su shẽƙẽwa

106Sa'an nan Yanã barin (wurinsu) faƙo mai santsi

107Bã ka ganin karkata a cikinsa, kuma bã ka ganin wani tudu

108A rãnar nan sunã biyar mai kira, bãbu karkata a gare shi, kuma sautuka suka yi kawaici ga Mai rahama, bã ka sauraren kõme fãce sautin tafiya

109A yinin nan cẽto bã ya yin amfãni fãce wanda Mai rahama Ya yi masa izni kuma Ya yarda da shi, da ya yi magana

110Yanã sanin* abin da ke a gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma bã su kẽwayẽwa da shi ga sani

111Kuma fuskõki suka ƙanƙan da kai ga Rãyayye, Tsayayye, alhãli kuwa wanda ya ɗauko wani zãlunci ya tãɓe

112Kuma wanda ya aikata wani abu daga ayyukan ƙwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bã ya tsõron wani zãlunci ko wata naƙasa

113Kuma haka Muka saukar da shi, Alƙur'ãni, yanã abin karantãwa, da Larabci kuma Muka jujjuya misãlai, a cikinsa, na tsõratarwa, tsammãninsu, sunã yin taƙawa ko ya sabbaba musu wata wa'aztuwa

114Sa'an nan Allah Mamallaki, Tabbatacce Yã ɗaukaka. Kuma kada ka yi gaggãwa* da Alƙur'ãni a gabãnin a ƙãre wahayinsa zuwa gare ka. Kuma ka ce: "Yã Ubangiji! Ka ƙãra mini ilmi

115Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun yi alkawari zuwa ga Ãdamu a gabãnin wannan, sai ya manta, kuma ba Mu sãmi ƙarfin zũciya a gare shi ba

116Kuma sa'ad da Muka ce wa malã'iku, "Ku yi sujada ga Ãdamu." Sai suka yi sujada, fãce Iblĩsa, yã ƙiya

117Sai Muka ce: "Ya Ãdamu! Lalle ne wannan maƙiyi* ne gare ka da kuma ga mãtarka, sabõda haka kada ya fitar da ku daga Aljanna har ku wahala

118Lalle ne kã sãmu bã zã ka ji yunwa ba a cikinta, kuma bã zã ka yi tsiraici ba

119Lalle kai, bã zã ka ji ƙishirwa ba, kuma bã zã ka shiga hantsi ba

120Sai shaiɗan ya sanya waswãsi zuwa gare shi, ya ce: "Yã Ãdamu! Shin, in shiryar da kai ga itãciyar dawwama da mulki wanda bã ya ƙãrẽwa

121Sai suka ci daga gare ta, sabõda haka al'aurunsu suka bayyana, kuma suka shiga sunã lulluɓãwa a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ãdamu ya sãɓã wa Ubangijinsa, sabõda haka ya ɓace

122Sa'an nan kuma Ubangjinsa Ya zãɓẽ shi, Ya karɓi tũba gare shi, kuma Ya shiryar (da shi)

123Ya ce: "Ku sauka kũ biyu daga gare ta gabã ɗaya, sãshenku yanã maƙiyi ga sãshe. To, imma dai wata shitiya ta jẽ muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiryarwãta, to, bã ya ɓacẽwa, kuma bã ya wahala

124Kuma wanda ya bijire* daga ambatõNa (Alƙur'ãni) to, lalle ne rãyuwa mai ƙunci ta tabbata a gare shi, kuma Munã tãyar da shi a Rãnar ¡iyãma yanã makãho

125Ya ce: "Ya Ubangiji! Don me Ka tãyar da ni makãho alhãli kuwa nã kasance mai gani

126Ya ce: "Kamar wancan ne ãyõyin Mu suka jẽ maka sai ka mance su, kuma kamar hakar a yau ake mance ka

127Kuma kamar haka Muke sãka wa wanda ya yawaita,* kuma bai yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinsa ba. Kuma lalle ne azãbar Lãhira ce mafi tsanani, kuma mafi wanzuwa

128Shin, to, bai shiryar da su ba cẽwa da yawa Muka halakarda (kãfirai) daga ƙarnuka, a gabãninsu, sunã tafiya a cikin masaukansu? Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu hankula

129Kuma bã dõmin wata kalma ba wadda ta gabãta daga Ubangijinka, da kuma ajali ambatacce haƙĩƙa, dã azãbarta kasance mai lazimta

130Sai ka yi haƙuri* a kan abin da suke cẽwa, kuma ka yi tasbĩhi da gõdẽ wa Ubangijinka a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta, kuma daga sã'õ'in dare sai ka yi tasbĩhi da sãsannin yini, tsammãninka zã ka sãmi yarda

131Kuma kada ka mĩƙar da idãnunka zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi da shi, nau'i-nau'i daga gare su, kamar huren rãyuwar dũniya yake, dõmin Mu fitine su a cikin sa, alhãli kuwa arzikin Ubangijinka, ne mafi alhẽri kuma mafi wanzuwa

132Kuma ka umurci iyãlanka da salla, kuma ka yi haƙuri a kanta. Bã Mu tambayar ka wani Arziki Mu ne Muke azurta ka. Kuma ãƙiba mai kyau tanã ga taƙawa

133Kuma suka ce: "Don me bã ya zo mana da wata ãyã daga Ubangijinsa?" Shin, kuwa hujjar abin da ke a cikin littattafan farko, ba ta jẽ musu ba

134Kuma dã dai Mun halaka sũ da wata azãba daga gabãninsa, lalle ne dã sun ce: "Yã Ubangijinmu! Dã Kã aiko da wani Manzo zuwa gare mu har mu bibiyi ãyõyinKa daga gabãnin mu ƙasƙanta, kuma mu wulãkantu

135Ka ce: "Kõwa mai tsumãye ne. Sai ku yi tsumãye. Sa'an nan zã ku san su wa ne ma'abũta tafarki madaidaici, kuma wane ne ya nẽmi shiryuwa

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath