Musulunci
baya

98. Al-Bayyina

1Waɗanda suka kãfirta daga mũtanen Littafi, da mushirikai, ba su kasance masu gushewa daga gaskiya ba har hujja ta je musu

2Wani Manzo* daga Allah, yana karatun wasu takardu masu tsarki

3A cikinsu akwai wasu littafai mãsu ƙĩma da daraja

4Kuma waɗanda aka bai wa Littafi ba su sãɓa wa juna ba face bayan hujjar ta je musu

5Kuma ba a umarce su da kome ba fãce bauta wa Allah suna mãsu tsarkake addinin gare Shi, mãsu karkata zuwa ga addinin gaskiya, kuma su tsai da salla kuma su bãyar da zakka, kuma wannan shi ne addinin waɗanda suke a kan hanyar ƙwarai

6Lalle ne waɗanda suka kafirta daga mutanen Littafi da mushirikai sana cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta. Waɗannan su ne mafi ashararancin tãlikai

7Lalle ne waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan su ne mafifita alherin halitta

8Sakamakonsu, a wurin Ubangijinsu, shi ne gidajen Aljannar zama, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã madawwama a cikinta har abada. Allah Ya yarda da su, kuma su, sun yarda da Shi. wannan sakamako ne ga wanda ya ji tsõron Ubangijinsa

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath