96. Al-Alaq
1Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta
2Ya hahitta mutum daga gudan jini
3Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne Mafi karimci
4Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami
5Ya sanar da mutum abin da bai sani ba
6A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu)
7Dõmin yã ga kansa, yã wadãta
8Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take
9Shin, kã ga wanda ke hana
10Bãwã idan yã yi salla
11Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya
12Ko ya yi umurni da taƙawa
13Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya
14Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani
15A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa
16Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi
17Sai ya kirayi ƙungiyarsa
18Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma)
19A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u,* kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka)
tushe: Abubakar Mahmood Jummi
WEBREATH · 11:11
«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath