Musulunci
baya

95. A-Tin

1Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn

2Da Dũr Sĩnĩna

3Da wannan gari* amintacce

4Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa

5Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni

6Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa

7To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)

8Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath