Musulunci
baya

92. Al-Lail

1Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa

2Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa

3Da abin da ya halitta namiji da mace

4Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke

5To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa

6Kuma ya gaskata kalma* mai kyãwo

7To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi

8Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa

9Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo

10To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani

11Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta)

12Lãlle aikin Mu ne, Mu bayyana shiriya

13Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne

14Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka

15Bãbu mai shigarta sai mafi Tabewa

16Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya

17Kuma mafi taƙawa* zai nisance ta

18Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka

19Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta

20Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka

21To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi)

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath