Musulunci
baya

91. Ash-Shams

1Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta

2Kuma da wata idan ya bi ta

3Da yini a lõkacin da ya bayyana ta

4Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta

5Da sama da abin da ya gina ta

6Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta

7Da rai da abin da ya daidaita shi

8Sa'an nan ya yi masa Ilhamar fãjircinsa da shiryuwarsa

9Lalle ne wanda ya tsarkake* shi (rai) ya sãmi babban rabo

10Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe* shi (da laifi) ya tãɓe

11Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu

12A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu)

13Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta

14Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi)

15Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar)

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath