Musulunci
baya

90. Al-Balad

1Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari* ba

2Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari

3Da mahaifi da abin da ya haifa

4Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala

5Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa

6Yana cẽwa "Na* halakarda dũkiya mai yawa

7Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba

8Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba

9Da harshe, da leɓɓa biyu

10Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi* biyu ba

11To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba

12Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã

13Ita ce fansar wuyan bãwa

14Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa

15Ga marãya ma'abũcin zumunta

16Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya

17Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi

18Waɗannan ne ma'abũta albarka

19Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Mu, sũ ne ma'abũta shu'umci

20A kansu akwai wata wuta abar kullewa

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath