Musulunci
baya

89. Al-Fajr

1Inã rantsuwa da alfijiri

2Da darũruwa gõma

3Da (adadi na) cikã da (na) mãrã

4Da dare idan yana shũɗewa

5Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)

6Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba

7Iramawa mãsu sakon* ƙĩrar jiki

8Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya)

9Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi* suka yi gidãje

10Da Fir'auna mai turãku

11Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa

12Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu

13Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba

14Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka

15To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni

16Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni

17A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya

18Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci

19Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa

20Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa

21A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai

22Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, sahu- sahu

23Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi

24Yana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata

25To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah

26Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurin Sa

27Yã kai rai mai natsuwa

28Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira)

29Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyi Na (mãsu bin umurui a dũniya)

30Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira)

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath