Musulunci
baya

88. Al-Ghaashiya

1Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka

2Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne

3Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya

4Zã su shiga wata wuta mai zãfi

5Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa

6Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi

7Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba

8Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne

9Game da aikinsu, masu yarda ne

10(Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya

11Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta

12A cikinta akwai marmaro mai gudãna

13A cikinta akwai gadãje maɗaukaka

14Da kõfuna ar'aje

15Da filõli* jẽre

16Da katifu shimfiɗe

17Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su

18Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta

19Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su

20Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta

21sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai

22Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba

23Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta

24To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma

25Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take

26Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath