Musulunci
baya

87. Al-A'la

1Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka

2Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar

3Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri)

4Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã

5Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa

6Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba

7Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye

8Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi

9Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni

10Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna

11Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta

12Wanda zai shiga wutar da tã fi girma

13Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba

14Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo

15Kuma ya ambaci sũnan* Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla

16Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya

17Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa

18Lalle ne, wannan* yanã a cikin littafan farko

19Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath