Musulunci
baya

86. At-Taariq

1Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare

2To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare

3Shi ne taurãron nan mai tsananin haske

4Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro

5To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi

6An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna

7Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji

8Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne

9Rãnar da ake jarrabawar asirai

10Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah)

11Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa

12Da ƙasa ma'abociyar tsãgẽwa

13Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki

14Kuma shĩ bã bananci* bane

15Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai

16Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi

17Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath