Musulunci
baya

85. Al-Burooj

1Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara

2Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa

3Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta* a cikinsa

4An la'ani mutãnen rãmi

5Wato wuta wadda aka hura

6A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune

7Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce

8Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa

9Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake

10Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara

11Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba

12Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai

13Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa)

14Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya

15Mai Al'arshi mai girma

16Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi

17Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka

18Fir'auna da samũdãwa

19Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa

20Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da sanin Sa)

21Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma

22A cikin Allo tsararre

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath