Musulunci
baya

83. Al-Mutaffifin

1Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa

2Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu

3Kuma idan sun auna musu da zakka* ko da sikẽli, suna ragẽwa

4Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba

5Domin yini mai girma

6Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta

7Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn

8Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn

9Wani ittãfi ne rubũtacce

10Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa

11Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako

12Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi

13Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne

14A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu

15A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne

16Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne

17Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi

18A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna

19Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna

20Wani littãfi ne rubũtacce

21Muƙarrabai* suke halarta shi

22Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima

23A kan karagu, suna ta kallo

24Kana sani a cikin fuskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima

25Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta

26¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma

27Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake

28(Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi

29Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya

30Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe

31Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci

32Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne

33Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu

34To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya

35A kan karagu, suna ta kallo

36Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath