Musulunci
baya

82. Al-Infitaar

1Idan sama ta tsãge

2Kuma idan taurãri suka wãtse

3Kuma idan tẽkuna aka facce su

4Kuma idan kaburbura aka tõne su

5Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar

6Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karamci

7Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka

8A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta

9A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako

10Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara

11Mãsu daraja, marubũta

12Sunã sanin abin da kuke aikatãwa

13Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima

14Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm

15Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako

16Bã zã su faku daga gare ta ba

17Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa ranar sakamako

18Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako

19Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath