Musulunci
baya

81. At-Takwir

1Idan rãna aka shafe haskenta

2Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani)

3Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su

4Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna* aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba

5Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su

6Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta

7Kuma idan rãyuka aka haɗa* su da jikunkunansu

8Kuma idan wadda aka turbuɗe* ta da rai aka tambaye ta

9Sabõda wane laifi ne aka kashe ta

10Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su)

11Kuma idan sama aka fẽɗe ta

12Kuma idan Jahĩm aka hũra ta

13Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita

14Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan)

15To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã* ba

16Mãsu gudu suna ɓũya

17Da dare idan ya bãyar da bãya

18Da sãfiya idan ta yi lumfashi

19Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah

20Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi

21Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce

22Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne

23Kuma lalle ne, yã gan shi* a cikin sararin sama mabayyani

24Kuma shi, ga gaibi* bã mai rowa ba ne

25Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce

26Shin, a inã zã ku tafi

27Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai

28Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu

29Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath