Musulunci
baya

80. Abasa

1Yã game huska* kuma ya jũya bãya

2Sabõda makãho yã je masa

3To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka

4Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi

5Amma wanda ya wadãtu da dũkiya

6Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi

7To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba

8Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa

9Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah

10Kai kuma kã shagala ga barinsa

11A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce

12Sabõda wanda ya so ya tuna Shi (Allah)

13(Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa

14Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa

15A cikin hannãyen mala'iku marubũta

16Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah

17An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa

18Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi

19Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye)

20Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa

21Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari

22Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi

23Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari)

24To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa

25Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa

26Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa

27Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta

28Da inabi da ciyãwa

29Da zaitũni da itãcen dabĩno

30Da lambuna, mãsu yawan itãce

31Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi

32Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku

33To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo

34Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa

35Da uwarsa da ubansa

36Da mãtarsa da ɗiyansa

37Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi

38Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne

39Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra

40Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu

41Baƙi zai rufe su

42Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu)

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath