Musulunci
baya

79. An-Naazi'aat

1Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi

2Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi

3Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo

4Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umarnin Allah) kamar suna tsẽre

5Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umarni

6Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa

7Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye

8Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne

9Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu

10Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu

11Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu

12Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya

13To, ita kam, tsãwa guda kawai ce

14Sai kawai gã su a bãyan ƙasa

15Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka

16A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã

17Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi

18Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka

19Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoron Sa

20Sai ya nũna masa ãyar* nan mafi girma

21Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni)

22Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri

23Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira

24Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka

25Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko

26Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah

27Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta

28Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta

29Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta

30Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta

31Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta

32Da duwatsu, Yã kafe ta

33Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku

34To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo

35Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata

36Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani

37To, amma wanda ya yi girman kai

38Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya)

39To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma

40Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai

41To, lalle ne Aljanna ita ce makõma

42Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta

43Me ya haɗã ka da ambatonta

44Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake

45Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta

46Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath