78. An-Naba
1A kan mẽ suke tambayar jũna
2A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)
3Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa
4A'aha! Zã su sani
5Kuma, a'aha! Zã su sani
6Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba
7Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)
8Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã
9Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa
10Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura
11Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci
12Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi
13Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)
14Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba
15Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi
16Da itãcen lambuna mãsu lillibniya
17Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci
18Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a
19Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi
20Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra
21Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata
22Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma
23Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna
24Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha
25Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini
26Sakamako mai dãcẽwa
27Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi
28Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyin Mu, ƙaryatãwa
29Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce
30Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba
31Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo
32Lambuna da inabõbi
33Da yan Mata tsaraikun Juna
34Da hinjãlan giya cikakku
35Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa
36Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa
37Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi
38Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai
39Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa
40Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya
tushe: Abubakar Mahmood Jummi
WEBREATH · 11:11
«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath