Musulunci
baya

77. Al-Mursalaat

1Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna

2Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi

3Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa

4sa'an nan, da ãyõyi* mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa

5Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni

6Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi

7Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne

8To, idan taurãri aka shãfe haskensu

9Kuma, idan sama aka tsãge ta

10Kuma, idan duwãtsu aka nike su

11Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su

12Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali

13Domin rãnar rarrabẽwa

14Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa

15Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa

16Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba

17Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe

18Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi

19Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa

20Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba

21Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce

22Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna

23Sa'an nan, Muka nũna iyãwar Mu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa

24Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa

25Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba

26Ga rãyayyu da matattu

27Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi

28Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa

29Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi

30Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku

31Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta

32Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye

33Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe

34Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa

35Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba

36Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari

37Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa

38Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko

39To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita

40Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa

41Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari

42Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari

43(A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa

44Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa

45Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa

46(Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne

47Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa

48Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba

49Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa

50To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath