75. Al-Qiyaama
1Bã sai Nã yi rantsuwa* da Rãnar ¡iyãma ba
2Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin* kansa ba
3Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba
4Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa
5Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa
6Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma
7To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli)
8Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe)
9Aka tãra rãnã da watã
10Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu
11A'aha! bãbu mafaka
12zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake
13Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar
14Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne
15Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba)
16Kada ka mõtsar* da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni)
17Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa
18To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa
19sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa
20A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne
21Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira)
22Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne
23Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne
24Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne
25Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso
26A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai
27kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada
28Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce
29Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri
30Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa* take
31To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba
32Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya
33Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama
34Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa
35Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa
36Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)
37Bai kasance ɗigo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)
38Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa
39Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace
40Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu
tushe: Abubakar Mahmood Jummi
WEBREATH · 11:11
«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath