Musulunci
baya

74. Al-Muddathhir

1Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi

2Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi

3Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi

4Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su

5Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu

6Kada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri

7Kuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure

8To, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho

9To, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya

10A kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne

11Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai

12Kuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya

13Da ɗiyã halartattu

14Kuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa

15Sa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri

16Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyin Mu, mai tsaurin kai

17Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa

18Lalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur'ãni)

19Sabõda haka, aka la'ane shi, kamar yadda ya ƙaddara

20Sa'an nan, aka la'ane shi kamar yadda ya ƙaddara

21Sa'an nan, ya yi tunãni

22Sa'an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk

23Sa'an nan, ya jũya bãya, kuma ya bunƙãsa

24Sai ya ce: "Wannan abu dai bã kõme ba ne fãce wani sihiri, wanda aka ruwaito

25Wannan maganar mutum dai ce

26Zã Ni ƙõna shi da Saƙar

27Kuma mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽwa Saƙar

28Bã ta ragẽwa, kuma bã ta bari

29Mai nãcẽwa ga jiki ce (da (ƙũna)

30A kanta akwai (matsara) gõma shã tara

31Kuma ba Mu sanya ma'abũta wutã (wãto matsaranta) ba, fãce malã'iku, kuma ba Mu sanya adadinsu (gõma sha tara) ba, fãce dõmin fitina ga waɗanda suka kãfirta domin waɗanda aka bai wa littãfi su sãmi yaƙĩni kuma waɗanda suka yi ĩmãni su ƙãra ĩmãni, kuma waɗanda aka bai wa littãfi da mũminai bã zã su yi shakka ba, kuma domin wa ɗanda a cikin zukatansu akwai wata cuta da kãfirai su ce: "Mẽ Allah Yake nufi da wannan, ya kasance misãli?" Haka dai Allah ke ɓatar da wanda Ya so, kuma Ya shiryar da wanda ya so. Kuma bãbu wanda ya san mayãƙan Ubangijinka fãce Shi, kuma ita (wutar) ba ta kasance ba fãce wata tunãtarwa ce ga mutum

32A'aha! Ina rantsuwa da watã

33Da dare a lõkacin da ya jũyar da baya

34Da sãfiya idan ta wãye

35Ita (wutar) ɗayan manyan masĩfũ? ce

36Mai gargaɗĩ ce ga mutum

37Ga wanda ya so, daga cikinku, ya gabãta ko ya jinkirta

38Kõwane rai ga abin da ya aikata jingina ce

39Fãce mutãnen dãma

40A cikin Aljanna suna tambayar jũna

41Game da mãsu laifi

42(Su ce musu) "Me ya shigar da ku a cikin Saƙar

43Suka ce: "Ba mu kasance munã a cikin mãsu salla ba

44Kuma ba mu kasance muna ciyar da matalautã ba

45Kuma mun kasance muna kũtsãwa tãre da mãsu kũtsãwa

46Mun kasance munã ƙaryata rãnar sãkamako

47Har gaskiya (wãto mutuwa) ta zo mana

48Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba

49Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya

50Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne

51Sun gudu daga zãki

52A'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa

53A'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira

54A'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce

55Dõmin wanda ya so, ya tuna

56Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath