71. Nuhu
1Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu
2Ya ce: "Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa
3Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõron Sa, kuma ku bĩ ni
4Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci)
5(Nũhu) ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini
6To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni)
7Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai
8Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane
9Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri
10Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne
11Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga
12Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna
13Me ya sãme ku, bã ku fãtar sãmun natsuwa daga Allah
14Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye
15Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba
16Ya sanya watã a cikinsu, yana mai haske, Ya sanya rãnã babbar fitila
17Kuma Allah Ya tsirar da ku daga ƙasa (kamar ganye) tsirarwa
18Sa'an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa
19Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa shimfidaɗɗiya
20Dõmin ku shiga a cikinta, hanyõyi mãsu fãɗi
21Nũhu ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne sũ sun saɓa mini sun bi wanda dukiyarsa da ɗiyansa ba su ƙãre shi da kõme ba sai da hasãra
22Kuma sun yi wani mãkirci, mãkirci babba
23Kuma suka ce: Faufau kada ku bar gumãkanku, kuma faufau, kada ku bar wadda, kuma kada ku bar suwã kuma kada ku bar Yagũsa da Yans uƙa da Nasra
24Kuma lalle ne sun ɓatar da (mutãne) mãsu yawa, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai (kõme) sai ɓata
25Sabõda laifukansu na ganganci aka nutsar da su, sa'an nan aka sanya su a wuta. Saboda haka ba su sãmã wa kansu wani mataimaki wanin Allah ba
26Kuma Nũhu ya ce: "Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kãfirai, wanda ke zama a cikin gida
27Lalle ne, Kai idan Ka bar su, zã su ɓatar da bãyin Ka, kuma bã zã su haifi kowa ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci
28Ya Ubanginjina! Ka yi mini gãfara (ni) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga gidana, yana mai ĩmãni, da mũminai maza da mũminai mãtã, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai kõme sai halaka
tushe: Abubakar Mahmood Jummi
WEBREATH · 11:11
«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath