70. Al-Ma'aarij
1Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa
2Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa
3Daga Allah Mai matãkala
4Malã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne
5Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo
6Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa
7Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa
8Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa
9Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi
10Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake
11Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa
12Da matarsa da ɗan'uwansa
13Da danginsa, mãsu tattarã shi
14Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi
15A'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã
16Mai twãle fãtar goshi
17Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai
18Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka
19Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi
20Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri
21Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa
22Sai mãsu yin salla
23Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne
24Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne
25Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon
26Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako
27Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro
28Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce
29Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne
30Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne
31To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka
32Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne
33Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne
34Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne
35Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne
36Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu)
37Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a
38Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)
39A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani
40Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne
41Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba
42Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita)
43Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa
44Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa)
tushe: Abubakar Mahmood Jummi
WEBREATH · 11:11
«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath