69. Al-Haqqa
1Kiran gaskiya
2Mẽne ne kiran gaskiya
3Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya
4Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya
5To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani
6Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi
7(Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi
8To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu
9Kuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi
10Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani)
11Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan
12Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi)
13To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya
14Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya
15A ran nan, mai aukuwa zã ta auku
16Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce
17Kuma malã'iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã'iku) takwas na ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar
18A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa
19To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karɓa, ku karanta littafina
20Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne
21Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda
22A cikin Aljanna maɗaukakiya
23Nunannun 'yã'yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba)
24(Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige
25Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba
26Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba
27In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce
28Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba
29Ĩkona ya ɓace mini
30(Sai a ce wa malã'iku) "Ku kãmã shi, sa'an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi
31Sa'an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi
32Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã'i saba'in, sai ku sanya shi
33Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma
34Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci
35Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi
36Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn
37Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci
38To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba
39Da abin da bã ku iya gani
40Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne
41Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata
42Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa
43Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka
44Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu
45Dã Mun kãma shi da dãma
46sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã
47Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbar Mu) daga gare shi
48Kuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa
49Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa
50Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai
51Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙini
52Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma
tushe: Abubakar Mahmood Jummi
WEBREATH · 11:11
«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath