Musulunci
baya

68. Al-Qalam

1Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa

2Kai, sabõda ni'imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba

3Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa

4Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya

5Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani

6Ga wanenku haukã take

7Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkin Sa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa

8Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa

9Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta

10Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce

11Mai zunɗe, mai yãwo da gulma

12Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi

13Mai girman kai, bãyan haka kuma la'ĩmi (bã ya son alhẽri)

14Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya

15Idan ana karanta masa ãyõyin Mu, sai ya ce: "Tatsũniyõyin mutãnen farko ne

16Zã Mu yi masa alãma a kan hanci

17Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci

18Kuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgẽwa

19Wani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, (ya ƙone ta,) alhãli sunã barci

20Sai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare

21Sai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci

22Cẽwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa

23Sai suka tafi sunã shãwara a ɓõye (sunã cẽwa)

24Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau

25Kuma suka yi sammako akan (niyyar) rõwa, matuƙar iyãwarsu

26Lõkacin da suka gan ta, sai suka ce: "Lalle, mun saki hanya (mun ɓace)

27Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne

28Mafificinsu (hankali) ya ce: "Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah

29Suka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai

30Sai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu

31Suka ce: "Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙẽtare iyãka

32Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ (ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne

33Haka dai azãbar* take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance zã su iya gãnẽwã

34Lalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni'ima

35Shin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa'a kamar mãsu laifi

36Me ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci (da haka)

37Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa

38Cẽwã kunã da, a cikinsa lalle (duk) abin da rãyukanku suka zãɓa

39Kõ kunã (riƙe) da wasu rantsuwõyin alkawari a kan Mu, har ya zuwa Rãnar ¡iyãma, cẽwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku

40Ka tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan (hukuncin)

41Kõ sunã da abõkan tãrẽwa (ga wannan ra'ayi)? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu, idan sun kasance mãsu gaskiya

42Ranar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujada, sai bã zã su iyãwa ba

43Su fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, (suka ƙi yi)

44Sabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri (Alƙur'ãni). Zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba

45Ina jinkirtã musu, lalle kaidi Na mai ƙarfi ne

46Kõ kana tambayar su wata la'ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin an nauyaya musu

47Ko kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun (abin da suke faɗã daga gare shi) ne

48Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma'abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi

49Ba dõmin ni'ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jẽfa shi a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi

50Sai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa'an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki

51Kuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da kallonsu (kallon mãmãki), a lokacin da suke jin karãtun Alƙur'ãni, kuma sunã cẽwa, "Lalle ne shi mahaukaci ne

52Shi (Alƙur'ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath