56. Al-Waaqia
1Idan mai aukuwa ta auku
2Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta
3(Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa
4Idan aka girgiza ƙasã girgizwa
5Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa
6Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa
7Kuma kun kasance nau'i uku
8Watau mazõwa dãma*. Mẽne ne mazõwa dãma
9Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu
10Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan
11Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar
12A ckin Aljannar ni'ima
13Jama'a ne daga mutãnen farko
14Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe
15(Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙu
16Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna
17Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu
18Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga
19Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa
20Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe
21Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa
22Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu
23Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye
24A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa
25Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi
26Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun
27Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma
28(Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya
29Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya
30Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya
31Da wani ruwa mai gudãna
32Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa
33Bã su yankẽwa kuma bã a hana su
34Da wasu shimfiɗu maɗaukaka
35Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa
36Sa'an nan Muka sanya su budurwai
37Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya
38Ga mazõwa dãma
39Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko
40Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe
41Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu
42Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi
43Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi
44Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba
45Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi
46Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma
47Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan
48Shin, kuma da ubanninmu na farko
49Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe
50Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne
51Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa
52Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)
53Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta
54Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi
55Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa
56Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako
57Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba
58Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi
59Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa
60Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa* ba
61A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba
62Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba
63Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa
64Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa
65Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki
66(Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra
67Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa
68Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha
69Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa
70Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa
71Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa
72Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa
73Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji
74Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma
75To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri
76Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani
77Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja
78A cikin wani littafi tsararre
79Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake
80Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta
81Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa
82Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)
83To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa)
84Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo
85Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani
86To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba
87Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya
88To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta
89Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima
90Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma
91Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma
92Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun
93Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi
94Da ƙõnuwa da Jahĩm
95Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni
96Sabõda haka, ka tsarkake* sũnan Ubangijinka, Mai karimci
tushe: Abubakar Mahmood Jummi
WEBREATH · 11:11
«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath