55. Ar-Rahman
1(Allah) Mai rahama
2Yã sanar da Alƙur'ani
3Yã halitta mutum
4Yã sanar da shi bayãni (magana)
5Rãnã da watã a kan lissãfi suke
6Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu'i
7Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli
8Dõmin kada ku karkatar da sikẽlin
9Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin
10Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai
11A cikinta akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa
12Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi
13To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangjinku *kuke ƙaryatãwa
14Yã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko
15Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã
16To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
17Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã
18To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
19Yã garwaya tẽku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa
20A tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba
21To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
22Lu'ulu'u da murjãni na fita daga gare su
23To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
24Kuma Yanã da manyan jirãge, waɗanda ake ƙãgãwa a cikin tẽku kamar manyan duwãtsu
25To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
26Dukkan wanda ke kanta* mai ƙãrẽwa ne
27Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa
28To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
29wanda ke a cikin sammai da ƙasã yanã rõƙon Sa (Allah), a kullum Allah na a cikin wani sha'ani
30To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
31Zã mu ɗauki lõkaci sabõda ku, yã kũ *mãsu nauyin halitta biyu
32To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
33Ya jama'ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya zarcẽwa daga sãsannin sammai da ƙasã to ku zarce. Bã za ku iya zarcẽwaba fãce da wani dalĩli
34To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
35Anã sako wani harshe daga wata wutã a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, bã zã ku nẽmi taimako ba
36To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
37Sa'an nan idan sama ta tsãge kuma ta zama jã kamar jar fãta
38To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
39To, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani
40To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
41zã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu
42To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
43Wannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita
44Sunã kẽwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa
45To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
46Kuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu
47To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
48Mãsu rassan itãce
49To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
50A cikinsu akwai marẽmari biyu sunã gudãna
51To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
52A cikinsu akwai nau'i biyu daga kõwane 'ya'yan itãcen marmari
53To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
54Sunã gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufãfin alharĩni mai kauri ne kuma nũnannun 'yã'yan itãcen Aljannar biyu kusakusa suke
55To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
56A cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani
57To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
58Kamar dai su yaƙũtu ne da murjãni
59To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
60Shin, kyautatãwa nã da wani sakamako? (Ã'aha) fãce kyautatãwa
61To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
62Kuma baicinsu akwai waɗansu gidãjen Aljanna biyu
63To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
64Mãsu duhun inuwa
65To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
66A cikinsu akwai marẽmari biyu masu kwarãrar ruwa
67To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
68A cikinsu akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno darummãni
69To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
70A cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyawun hãlãye, mãsu kyaun halitta
71To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
72Mãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi
73To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
74Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗẽbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani
75To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
76Sunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa
77To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
78Sũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka
tushe: Abubakar Mahmood Jummi
WEBREATH · 11:11
«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath