54. Al-Qamar
1Sã'a ta yi kusa, kuma wata *ya tsãge
2Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa
3Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi
4Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu
5Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni
6Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama
7¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse
8Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai wuya
9Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata Bawan Mu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi
10Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako
11Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba
12Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umarni da aka riga aka ƙaddara shi
13Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi
14Tanã gudãna, a kan idãnun Mu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin
15Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni
16To, yãyã azãbã Ta take da gargaɗi Na
17Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa
18Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗi Na
19Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa
20Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne
21To, yãya azãbã Ta take da gargaɗi Na
22Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa
23Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin
24Sai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã
25Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai
26Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan
27Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar* ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri
28Kuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa
29Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta
30To, yãya azãbaTa take da gargaɗi Na
31Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge
32Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa
33Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi
34Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba
35Sabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde
36Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙar Mu, sai suka yi musu game da gargaɗin
37Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. "To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩ Na
38Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe
39To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩ Na
40Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur, ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa
41Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna
42Sun ƙaryata game da ãyõyin Mu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi
43Shin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a cikin littattafai
44Kõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara
45Zã a karya* tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu
46Ã'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci
47Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka
48Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar
49Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri
50Kuma umurnin Mu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido
51Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni
52Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai
53Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne
54Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna
55A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa
tushe: Abubakar Mahmood Jummi
WEBREATH · 11:11
«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath