53. An-Najm
1Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku
2Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba
3Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa
4(Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa
5(Malã'ika) mai tsananin ƙarfi *ya sanar da shi
6Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita
7Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi daukaka
8Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa
9Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa
10Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa)
11Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba
12Shin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani
13Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa
14A wurin da magaryar tuƙẽwa take
15A inda taken, nan Aljannar makoma take
16Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta
17Ganinsa* bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba
18Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma* daga ãyõyin Ubangijinsa
19Shin, kun ga Lãta da uzza
20Da (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu
21Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace
22Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe
23Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar* ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton)
24Ko (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri
25To, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure)
26Akwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda
27Lalle waɗannan da bã su yin ĩmãni da Lãhira, haƙĩƙa sunã kiran malã'iku da sũnan mace
28Kuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya
29Sabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambaton Mu kuma bai yi nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya)
30Wannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyar Sa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya
31Kuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã na Allah kawai ne, dõmin Yã sãka wa waɗanda suka mũnana da abin da suka aikata, kuma Ya sãka wa waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau
32Waɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake* kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa
33Shin, ka ga wannan da ya jũya baya
34Ya yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa
35Shin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin
36Ko kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã
37Da Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari
38Cẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani
39Kuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata
40Kuma lalle, aikinsa zã a gan shi
41Sa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni
42Kuma lalle, makõmar zuwa Ubangijinka kawai take
43Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka
44Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar
45Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace
46Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa
47Kuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take
48Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar
49Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira
50Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko
51Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba
52Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai
53Da waɗanda aka birkice *ƙasarsu, Ya kãyar da su
54Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su
55To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake *yin shakka
56wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko
57Makusanciya* fa, tã yi kusa
58Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta
59Shin, kuma daga wannan *lãbãri kuke mãmãki
60Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka
61Alhãli kunã mãsu wãsã
62To, ku yi tawãli'u *ga Allah, kuma ku bauta (masa)
tushe: Abubakar Mahmood Jummi
WEBREATH · 11:11
«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath