Musulunci
baya

52. At-Tur

1Inã rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsã)

2Da wani littãfi rubũtacce

3A cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa

4Da Gidan da aka rãyar da shi (da ibãda)

5Da rufin nan da aka ɗaukaka

6Da tẽkun nan da aka cika (da ruwa)

7Lalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce

8Bã ta da mai tunkuɗẽwa

9Rãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo

10Kuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa

11To, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa

12Waɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã

13Rãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa

14(A ce musu): "Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita

15To, shin wannan sihiri ne kõ kuwa kũ ne bã ku gani

16Ku shigẽ ta. To, ku yi haƙuri ko kuma kada ku yi haƙuri, dai dai ne a kanku, kawai anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa

17Lalle, mãsu taƙawa, sunã a cikin gidãjen Aljanna da wata ni'ima

18Sunã mãsu jin dãɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsãre musu azãbar Jahĩm

19(A ce musu): "Ku ci, ku sha, da ni'ima, dõmin abin da kuka kasance kunã aikatãwa

20Sunã kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su waɗansu mãtã mãsu farin idãnu, mãsu girmansu

21Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma zũriyarsu *suka bĩ su ga ĩmãnin, Mun riskar da zũriyarsu da su, alhãli kuwa bã da Mun rage musu kõme ba daga aikinsu, kõwane mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta

22Kuma Muka yalwata musu 'ya'yan itãce da nãma irin wanda suke marmari

23Sunã mĩƙa wa jũnansu a cikinta hinjãlan giya, wadda bãbu yãsassar magana a cikinta, kuma bãbu jin nauyin zunubi

24Kuma waɗansu samãri nã gẽwayãwa a kansu, kamar dai sũ lu'ulu'u ne wanda ke kulle

25Waɗansunsu suka fuskanta zuwa ga waɗansu, sunã tambayar jũna

26Suka ce: "Lalle mũ mun kasance a gabãnin wannan (a dũniya) a cikin iyãlanmu munã jin tsõro

27To, Allah Yã yi mana kyautar falala, kuma Yã tsare mana azãbar iskar zãfi

28Lalle mũ mun kasance, a gãbanin haka, munã kiran sa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai kyautatãwa, Mai rahama

29To, ka tunãtar kai fa sabõda ni'imar Ubangjinka, bã bõka kake ba, kuma bã mahaukaci ba

30Shin zã su ce: "Mawãƙi ne, munã jiran, masĩfun mutuwa game da shĩ

31Ka ce: "Ku yi jira, domin nĩ ma lalle inã a cikin mãsu jira tãre da ku

32Shin, hankulansu ne ke umarin su da wannan, kõ kuwa sũ wasu mutãne ne mãsu ƙetare haddi

33Shin, cẽwa suke yi: "Shi ne ke ƙãga faɗarsa"? Ã'a ba su dai yi ĩmãni ba

34Sai su zõ da wani lãbãri mai misãlinsa idan sun kasance sũmãsu gaskiya ne

35Shin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta

36Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba

37Shin, taskõkin Ubangijinka, sunã a wurinsu ne? Kõ kuwa sũ ne mãsu rinjãya

38Shin, sunã da wani tsãni ne wanda suke (hawa sunã) saurãron (lãbãrin samã) a cikinsa? Sai mai saurarõnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne

39Shin, Yanã da* 'ya'ya mãtã ne kuma kũ, kunã da ɗiya maza ne

40Shin, kanã tambayar su wata ijãra ne, sabõda haka suka zama mãsu jin nauyin biyan tãrar

41Shin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabõda haka sunã rubũtãwa

42Shin, sunã nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kãfirta sũ ne waɗanda ake yi wa kaidi

43Shin, sunã da wani abin bautãwa ne wanda bã Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke yi na shirki

44Kuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samã yãnã fãɗuwa, sai su ce wani girgije ne, mai hauhawar jũna

45To, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa

46Rãnar da kaidinsu bã ya wadãtar masu da kõme, kuma bã a taimakon su

47Kuma lalle, waɗannan da suka yi zãluncin, sunã da azãba (a nan dũniya) banda waccan, kuma mafi yawansu ba su sani ba

48Sai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kanã idãnun Mu, kuma ka tsarkake* Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gõde Masa a lõkacin da kake tãshi tsaye (dõmin salla kõ wani abu)

49Kuma daga dare, sai ka tsarkake Shi (da tasbĩhin) da lõkacin jũyãwar taurãri

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath