Musulunci
baya

51. Adh-Dhaariyat

1Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa

2Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa)

3Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi

4Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah)

5Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne

6Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne

7Inã rantsuwa da samã ma'abũciyar hanyõyi (na tafiyar taurãri da sautin rediyo)

8Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur'ani)

9Anã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya)

10An la'ani mãsu ƙiri-faɗi

11Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci

12Sunã tambaya: "Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku

13Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su

14(A ce musu): "Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa

15Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari

16Sunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bã su. Lalle sũ, sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka (a dũniya)

17Sun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci

18Kuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri

19Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo

20Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni

21Kuma a cikin rãyukanku (akwai ãyõyi). To, bã zã ku dũbã ba

22Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari

23To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ (abin da ake yi muku alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana

24Shin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka

25A lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce "Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi

26Sai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna

27Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: "Bã zã ku ci ba

28Sai ya ji tsõro daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro." Kuma suka yi masa bushãra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi

29Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: "Tsõhuwa bakarãriya (zã ta haihu)

30Suka ce: "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi

31(Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni

32Suka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi

33Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom)

34Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna

35Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai

36Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi

37Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi

38Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne

39Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci

40Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi

41Kuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu

42Bã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa

43Kuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci

44Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo

45Ba su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman ãgaji ba

46Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai

47Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa

48Kuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ

49Kuma daga kõme Mun halitta nau'i biyu, watakila zã ku yi tunãni

50Sabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi

51Kuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi

52Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: "Mai sihiri ne kõ mahaukaci

53shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai

54Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne

55Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai

56Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini

57Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni

58Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi

59To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa

60Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath