50. Kaf
1Inã rantsuwa da Alƙur'ãni Mai girma
2Ã'a, sun yi mãmãki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, yã zo musu, sai kãfirai suka ce: "Wannan wani abu ne mai ban mãmãki
3Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓãya (zã a kõmo da mu)? Waccan kõmowa ce mai nĩsa
4Lalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragẽwo daga gare su, kuma wurin Mu akwai wani littãfi mai tsarẽwa
5Ã'a, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lõkacin da ta je musu, sabõda haka sunã a cikin wani al'amari mai raurawa
6Shin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga samã a bisa gare su, yadda Muka gĩna ta, kuma Muka ƙawãce ta, kuma bã ta da waɗansu tsãgogi
7Da ƙasã, Mun mĩƙe ta, kuma Mun jẽfa kafaffun duwãtsu a cikinta, kuma Mun tsirar, a cikinta daga kõwane ma'auri mai ban sha'awa
8Dõmin wãyar da ido da tunãtarwa ga dukan bãwa mai tawakkali
9Kuma Mun sassakar, daga samã ruwa mai albarka sa'an nan Muka tsirar game da shi (itãcen) lambuna da ƙwãya abin girbẽwa
10Da itãcen dabĩno dõgãye, sunã da'ya'yan itãce gunda mãsu hauhawar jũna
11Dõmin arziki ga bãyi, kuma Muka rãyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar wannan ne fitar daga kabari kake
12Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu (mutãnen yanzu) da ma'abũta Rassi, *da Samũdãwa
13Da Ãdãwa da Fir'auna da 'yan'uwan Lũɗu
14Da ma'abũta ƙunci *da mutãnen Tubba'u,** kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacẽwaTa ta tabbata
15Shin, to, Mun kãsa ne game da halittar farko? Ã'a, su sunã a cikin rikici daga halitta sãbuwa
16Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar hannayẽnsa
17A lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani (malã'ika) zaunanne
18Bã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce
19Kuma mãyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare shi kanã bijirẽwa
20Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa
21Kuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida
22(Sai a ce masa): "Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, sabõda haka ganinka a yau, mai kaifi ne
23Kuma abõkin haɗinsa* ya ce: "Wannan shi ne abin da ke tãre da ni halarce
24(A ce wa Malã'iku), "Ku jẽfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kãfirci, mai tsaurin rai
25Mai yawan hanãwa ga alhẽri, mai zãlunci, mai shakka
26Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujẽfa shi a cikin azãba mai tsanani
27Abõkin haɗinsa* ya ce: "Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa
28Ya ce: "Kada ku yi husũma a wur Nalhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku
29Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyi Na
30Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe,* akwai wani ƙãri
31Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba
32Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa)
33Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, *kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali
34(A ce musu) "Ku shige ta da aminci, *waccan ita ce rãnar dawwama
35Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni'ima
36Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi, (waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: 'Kõ akwai wurin tsĩra'?* (Babu)
37Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa)
38Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata'yar wahala ba ta shãfe Mu ba
39Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi* game da gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta
40Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada
41Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri *makusanci
42Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari)
43Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take
44Rãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu
45Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur'ani,* ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa
tushe: Abubakar Mahmood Jummi
WEBREATH · 11:11
«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath