Musulunci
baya

37. As-Saffaat

1Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi)

2Sa'an nan mãsu yin tsãwa* dõmin gargaɗi

3Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa

4Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne

5Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã

6Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri

7Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai

8Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe

9Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya

10Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi

11Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri

12Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili

13Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa

14Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili

15Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne

16Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne

17Ashe kõ da ubanninmu na farko

18Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu

19Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi

20Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako

21Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa

22Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa

23Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm

24Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne

25Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna

26Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne

27Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna

28Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)

29Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba

30Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka

31Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne

32Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu

33To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar

34Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi

35Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai

36Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci

37Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni

38Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne

39Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa

40Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake

41Waɗannan sunã da abinci sananne

42Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa

43A cikin gidãjen Aljannar ni'ima

44A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna

45Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari

46Farã mai dãɗi ga mashãyan

47A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba

48Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu

49Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye

50Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna

51Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)

52Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne

53Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne

54(Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)

55Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim

56Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni

57Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)

58Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba

59Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba

60Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma

61Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa

62Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm

63Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai

64Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm

65Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne

66To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta

67Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi

68Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take

69Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu

70Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa

71Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu

72Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu

73Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance

74Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake

75Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu

76Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba

77Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa

78Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe

79Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu

80Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa

81Lalle shi, yanã daga bãyin Mu mũminai

82Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu

83Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake

84A lõkacin da ya je wa ubangijinsa da zũciya kuɓutacciya

85A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa

86Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa

87To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu

88Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri

89Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne

90Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya

91Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba

92Me ya sãme ku, bã ku magana

93Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma

94Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa

95Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa

96Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa

97Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm

98Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci

99Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni

100Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne

101Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro *mai haƙuri

102To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri

103Yayin da suka mika wuya sai muka fansheshi da Rago

104Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm

105Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa

106Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna

107Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma

108Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe

109Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm

110Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa

111Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai

112Kuma Muka yi masa bushãra* Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne

113Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin)

114Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna

115Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma

116Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya

117Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni

118Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya

119Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe

120Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna

121Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa

122Lalle, sunã daga bãyin Mu mũminai

123Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni

124A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba

125Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta

126Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko

127Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã)

128Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake

129Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe

130Aminci ya tabbata ga Ilyãs

131Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa

132Lalle shĩ, yanã daga bãyin Mu mũminai

133Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni

134A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya

135Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba)

136Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen

137Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci

138Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba

139Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni

140A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi

141Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya

142Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi

143To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba

144Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su

145Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya

146Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi

147Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka)

148Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci

149Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza

150Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce

151To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa

152Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne

153Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza

154Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannan hukunci)

155Shin, bã ku tunãni

156Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne

157To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya

158Kuma suka sanya nasaba a tsakãnin Sa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã)

159Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa

160Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake

161To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa

162Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi

163Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm

164Kuma bãbu kõwa daga cikinmu,* fãce yanã da matsayi sananne

165Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)

166Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi

167Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa

168Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko

169Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake

170Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani

171Kuma lalle, haƙĩƙa kalmar Mu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni

172Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako

173Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya

174Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci

175Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani

176Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa

177To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana

178Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci

179Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa

180Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa

181Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni

182Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath