26. Ash-Shu'araa
1S̃. M̃
2Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne
3Tsammãninka kai mai zaka halakar da ranka ne, dõn ba su zamanto mũminai ba
4Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai
5Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa
6To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu
7Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau
8Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba
9Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama
10Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, "Ka je wa mutãnen nan azzãlumai
11Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba
12Ya ce: "Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni
13Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci* kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa ga Harũna
14Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni
15Ya ce: "Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre
16Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne
17Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu
18Ya ce: "Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka
19Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai
20Ya ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin fushi
21Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni
22Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla
23Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu
24Ya ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni
25Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, "Bã za ku saurãra ba
26Ya ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko
27Ya ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne
28Ya ce: "Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta
29Ya ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru
30Ya ce: "Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa
31Ya ce: "To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya
32Sai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne
33Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo
34(Fir'auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, "Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci ne, mai ilmi
35Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa
36Suka ce: "Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne
37Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani
38Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne
39Kuma aka ce wa mutãne "Kõ kũ mãsu tãruwã ne
40Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya
41To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna,"Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya
42Ya ce: "Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai
43Mũsã ya ce musu, "Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa
44Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya
45Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya
46Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada
47Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta
48Ubangijin Mũsa da Hãrũna
49Ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne haƙĩƙa, zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku gabã ɗaya
50Suka ce: "Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu
51Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun kasance farkon mãsu ĩmãni
52Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã* ne
53Sai Fir'auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne
54Lalle ne, waɗannan, haƙĩƙa, ƙungiya ce kaɗan
55Kuma lalle ne sũ, a gare Mu, Mãsu fusãtarwa ne
56Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa gabã ɗaya mãsu sauna ne
57Sai Muka fitar da su daga gonaki da marẽmari
58Da taskõki da mazauni mai kyau
59Kamar haka! Kuma Muka gãdar da su ga Banĩ Isrãĩla
60Sai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã
61Sa'an nan a lõkacin da jama'a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: "Lalle ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne
62Ya ce: "Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni
63Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa "Ka dõki tẽku da sandarka." Sai tẽku ta tsãge,* kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma
64Kuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can
65Kuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya
66Sa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen
67Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba
68Kuma lalle ne Ubangijinka, kaƙĩƙa, Shĩ ne Mabũwayi, Mai jin ƙai
69Kuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm
70A sã'ilin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bauta wa
71Suka ce: "Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su
72Ya ce: "Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira
73Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku
74Suka ce: "Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa
75Ya ce: "Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa
76Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa
77To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu
78Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni
79Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni
80Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni
81Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni
82Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako
83Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai
84Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya* a cikin mutãnen ƙarshe
85Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima
86Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu
87Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su
88A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi
89Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki
90Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa
91Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku
92Kuma aka ce musu, "Inã abin da kuka kasance kunã bautawa
93Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu
94Sai aka kikkife su* a cikinta, su da halakakkun
95Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya
96Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma
97Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna
98A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu
99Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi
100Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta
101Kuma bã mu da abõki, masõyi
102Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai
103Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba
104Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai
105Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni
106A lõkacin da Dan uwansu Nuhu ya ce musu, "Bã zã ku ji tsoron Allah ba
107Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce
108To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã
109Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu
110Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã
111Suka ce: "Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka
112Ya ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa
113Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa
114Ban zama mai kõre mũminai ba
115Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa
116Suka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa
117Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni
118Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai
119Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi
120Sa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran
121Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba
122Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama
123Ãdãwa sun ƙaryata Manzanni
124A lõkacin da ɗan'uwansu, Hũdu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba
125Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce
126Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã
127Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu
128Shin, kunã yin ginin sitadiyo* a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa
129Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama
130Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa
131To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã
132Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani
133Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya
134Da gõnaki da marẽmari
135Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma
136Suka ce: "Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba
137Wannan abu bai zamõ ba fãce hãlãyen* mutãnen farko
138Kuma mũ ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba
139Sabõda haka suka ƙaryata shi, sai Muka halakar da sũ. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba
140Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai
141Samũdãwa sun ƙaryata Manzanni
142A lõkacin da ɗan'uwansu Sãlihu ya ce: "Shin, bã zã ku bi Allah da taƙawa ba
143Lalle ne nĩ zuwã gare ku, Manzo ne, amintacce
144Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã
145Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba fãce da a Ubangijin halittu
146Shin, anã barin ku* a cikin abin da yake a nan, kunã amintattu
147A cikin gõnaki da marẽmari
148Da shuke-shuke da dabĩ nai, 'ya'yan itãcensu hirtsi* mãsu narkẽwa a ciki
149Kuma kunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, kunã mãsu alfãhari
150Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã
151Kada ku yi ɗã'ã ga umurnin maɓarnata
152Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma bã su kyautatãwa
153Suka ce: "Kai daga mãsu sihiri kurum kake
154Bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu. To, kã zo da wata ãyã idan kã kasance daga mãsu gaskiya
155Ya ce: "Wannan rãkuma ce tanã da shan* yini, kuma kunã da shan yini sasanne
156Kada ku shãfe ta da cũta har azãbar yini mai girmã ta shãfe ku
157Sai suka sõke ta sa'an nan suka wãyi gari sunã mãsu nadãma
158Sabõda haka azãba ta kãma su. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba
159Lalle ne Ubangijinka, haƙĩ ƙa, Shĩ ne Mabuwayi, Mai jin ƙai
160Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata Manzanni
161A lõkacin da ɗan'uwansu,* Lũɗu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba
162Lalle ne nĩ, zuwa gare ku, Manzõ ne, amintacce
163Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã
164Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu
165Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai
166Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa
167Suka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)
168Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa
169Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa
170Sabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya
171Fãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa
172Sa'an nan kuma Muka hallaka wasu
173Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana
174Lalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba
175Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai
176Ma'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni
177A lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba
178Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce
179Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã
180Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu
181Ku cika mũdu, kuma kada ku kasance daga mãsu sanyãwar hasãra (ga mutãne)
182Kuma ku yi awo da sikẽli daidaitacce
183Kuma kada ku nakasa wa mutãne abũbuwansu kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa kuna mãsu ɓarna
184Kuma ku ji tsõron Allah wanda Ya halitta ku, kũ da jama'ar farko
185Suka ce: "Kai dai daga waɗanda suke sihirtattu kawai ne
186Kuma bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu kuma lalle ne munã zaton ka, haƙĩƙa, daga maƙaryata
187To ka jẽfo wani ɓaɓɓake daga sama a kanmu, idan ka kasance daga mãsu gaskiya
188Ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga abin da kuke aikatãwa
189Sai suka ƙaiyatã shi, sabõda haka, azãbar rãnar girgije* ta kãma su. Lalle ne ita, tã kasance azãbar yini mai girma
190Lalle a cikin wancan haƙĩka akwai ãya, amma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba
191Kuma lalle Ubangijĩnka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai
192Kuma lalle shi (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, saukarwar Ubangijinhalittu ne
193Rũhi* amintacce ne ya sauka da shi
194A kan zũciyarka, dõmin ka kasance daga mãsu gargaɗi
195Da harshe na Larabci mai bayãni
196Kuma lalle shin, haƙĩƙa, yanã a cikin litattafan (Manzannin) farko
197Ashe, bai kasance ãyã ba a gare su, ya zama Mãlaman Banĩ Isrã'ĩla sun san shi
198Kuma dã mun saukar da shi a kan sãshen Ajamãwa
199Ya karanta shi a kansu, ba su kasance sabõda shi mãsu ĩmãni ba
200Kamar wancan ne! Muka shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi
201Bã zã su yi ĩmãni da shĩ ba sai sun ga azãbar nan mai raɗadi
202Sai ta taho musu kwatsam, alhãli kuwa sũ, ba su sansance ba
203Sai su ce: "Shin, mu waɗanda ake yi wa jinkiri ne
204Ashe, to, da azãbar Mu suke nẽman gaggãwa
205Ashe, to, kã gani, idan Muka jĩshe su daɗi a shẽkaru
206Sa'an nan abin da suka kasance anã yi musu wa'adi (da shi) ya jẽ musu
207Abin da suka kasance anã jĩshe su dãɗin bã zai tunkuɗe azãba ba daga gare* su
208Kuma bã Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da mãsu gargaɗi
209Dõmin tunãtarwa, kuma ba Mu kasance Mãsu zãlunci ba
210Kuma (Alƙur'ãni) Shaiɗãnu ba su ɗõra sauka da shĩba
211Kuma bã ya kamãta a gare su (su Shaiɗãnu su sauka da shi), kuma ba su iyãwa
212Lalle ne sũ, daga saurãre, haƙĩƙa, waɗanda aka nĩsantar ne
213Sabõda haka, kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah, sai ka kasance daga waɗanda ake yi wa azãba
214Kuma ka yi gargaɗi ga danginka mafiya kusanci
215Kuma ka sassauta fikãfikanka* ga wanda ya bĩ ka daga mũminai
216Sa'an nan idan suka sãɓã maka to ka ce: "Lalle nĩ, barrantacce ne daga abin da kuko aikatãwa
217Kuma ka dõgara ga Mabuwãyi, Mai jin ƙai
218Wanda Yake ganin ka a lõkacin da kake tãshi tsaye
219Da jujjuyãwarka a cikin mãsu yin sujada
220Lalle Shi, Shi* ne Mai ji, Masani
221Shin, (kunã so) in gaya* muku a kan wanda Shaiɗãnnu kan sauka
222Sukan sauka a kan dukkan maƙaryaci, mai zunubi
223Sunã jẽfa (abin da suka) ji, alhãli kuwa mafi yawansu maƙaryata ne
224Kuma mawãƙa* halakakku ne ke bin su
225Shin, ba ku cẽwa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin ɗimuwa (su ƙẽtare haddi) ba
226Kuma lalle ne, sũ, sunã faɗin abin da bã su aikatãwa
227Fãce waɗanda suka yi ĩmãni suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rãma zãlunci, daga bãyan an zãlunce su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa
tushe: Abubakar Mahmood Jummi
WEBREATH · 11:11
«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath