Musulunci
baya

15. Al-Hijr

1L̃.R. Waɗan can ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa

2Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi

3Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani

4Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne

5Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba

6Suka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne

7Dõmin me bã zã ka zo mana da malã'ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya

8Bã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya,* bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba

9Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lale Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi

10Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãnin ka

11Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi

12Kamar wancan ne Muke shigar da shi* a cikin zukãtan mãsu laifi

13Bã su yin ĩmãni da shi,(4( kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige)

14Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa

15Lalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce

16Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo

17Kuma Muka kiyãye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa

18Fãce wanda ya sãci saurãre sai wutar yũlã bayyananniya ta bĩ shi

19Kuma ƙasa Mun mĩkẽ ta kuma Mun jẽfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikẽli

20Kuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã* da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba

21Kuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne

22Kuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa'an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacẽwa a gare shi ba

23Kuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashẽwa kuma Mũ ne magada

24Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri

25Kuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani

26Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja

27Kuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabãni, daga wutar* iskar zafi

28Kuma a lõkacin da Ubangijinka ya ce wa malã'iku: "Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja

29To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa* a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada

30Sai malã'iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya

31Fãce Iblĩs, ya ƙi kasancẽwa daga mãsu yin sujadar

32Ya ce: "Yã Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba

33Ya ce: "Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja

34Ya ce: "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne

35Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako

36Ya ce: "Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su

37Ya ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri

38Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sanan ne

39Ya ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya

40Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake

41Ya ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici

42Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu

43Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'akawartarsu gabã ɗaya

44Tanã da ƙõfõfi bakwai,* ga kõwace ƙõfa akwai wani juz'i daga gare su rababbe

45Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa

46Ku shigẽ ta da aminci, kunã amintattu

47Kuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama 'yan'uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã

48Wata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga, cikin ta ba

49Ka bai wa bãyiNa lãbari cẽwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai

50Kuma azãbãTa ita ce Azãba mai raɗaɗi

51Kuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm

52A lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: "Sallama." Ya ce: "Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne

53Suka ce: "Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi makabushãra game da wani yãro masani

54Ya ce: "Shin kun bã ni bushãra* ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara

55Suka ce: "Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni

56Ya ce: "Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijin sa, fãce ɓatattu

57Ya ce: "To, mẽne ne babban al'amarinku? Yã kũ manzanni

58Suka ce: "Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi

59Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya

60Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka

61To, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu

62Ya ce: "Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba

63Suka ce: "Ã'a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa

64Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne

65Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku

66Kuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga Asuba

67Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra

68Ya ce: "Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni

69Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki

70Suka ce: "Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba

71Ya ce: "Ga waɗannan, 'ya'yãna* idan kun kasance mãsu aikatãwa ne

72Rantsuwa da* rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa

73Sa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã

74Sa'an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu

75Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali

76Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya

77Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni

78Kuma lalle ne ma'abũta Al'aika* sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci

79Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani

80Kuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri* sun ƙaryata Manzanni

81Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su

82Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu

83Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga Asuba

84Sa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba

85Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau

86Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani

87Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗan da ake maimaita karatunsu* da Alƙur'ãni mai girma

88Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni

89Kuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyanan ne

90Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa

91Waɗanda suka sanya Alƙur'ãni tãtsuniyõyi

92To, rantsuwa da Ubangijinka!* Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya

93Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa

94Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki

95Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu* izgili

96Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa'an nan da sannu zã su sani

97Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili)

98Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada

99Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath