Musulunci
baya

104. Al-Humaza

1Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa)

2Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa

3Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi

4A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama

5Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama

6Wutar Allah ce wadda ake hurawa

7Wadda take lẽƙãwa a kan zukata

8Lalle ne ita abar kullẽwa ce a kansu

9A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu

tushe: Abubakar Mahmood Jummi

WEBREATH · 11:11

«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath