101. Al-Qaari'a
1Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)
2Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa
3Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa
4Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa
5Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe
6To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi
7To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda
8Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi)
9To, uwarsa Hãwiya ce
10Kuma me ya sanar da kai mece ce ita
11Wata wuta ce mai kuna
tushe: Abubakar Mahmood Jummi
WEBREATH · 11:11
«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath