100. Al-Adiyat
1Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki
2Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa
3Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba
4Sai su motsar da ƙũra game da shi
5Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya
6Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa
7Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa da haka
8Kuma alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne
9Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura
10Aka bayyana abin da ke cikin zukata
11Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne
tushe: Abubakar Mahmood Jummi
WEBREATH · 11:11
«If you are thankful, I will give you more» — Quran 14:7
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath