Waƙar Waƙoƙi 1
1Waƙar Waƙoƙin Solomon.
2Bari yă sumbace ni da sumbar bakinsa, gama ƙaunarka ta fi ruwan inabi zaƙi.
3Ƙanshin turarenka mai daɗi ne; sunanka kuwa kamar turaren da aka tsiyaye ne. Shi ya sa mata suke ƙaunarka!
4Ka ɗauke ni mu gudu, mu yi sauri! Bari sarki yă kai ni gidansa. Ƙawaye Muna farin ciki muna kuma murna tare da kai, za mu yabi ƙaunarka fiye da ruwan inabi. Ƙaunatacciya Daidai ne su girmama ka!
5Ni baƙa ce, duk da haka kyakkyawa. Ya ku ’yan matan Urushalima, ni baƙa ce kamar tentunan Kedar, kamar labulen tentin Solomon.
6Kada ku harare ni domin ni baƙa ce, gama rana ta dafa ni na yi baƙa. ’Ya’yan mahaifiyata maza sun yi fushi da ni suka sa ni aiki a gonakin inabi; na ƙyale gonar inabi na kaina.
7Faɗa mini, kai da nake ƙauna, ina kake kiwon garkenka kuma ina kake kai tumakinka su huta da tsakar rana. Me ya sa zan kasance kamar macen da aka lulluɓe kusa da garkunan abokanka?
8Ke mafiya kyau a cikin mata, in ba ki sani ba, to, ki dai bi labin da tumaki suke bi ki yi kiwon ’yan awakinki kusa da tentunan makiyaya.
9Ina kwatanta ke ƙaunatacciyata, da goɗiya mai jan keken yaƙin kayan Fir’auna.
10’Yan kunne sun ƙara wa kumatunki kyau, wuyanki yana da jerin kayan wuya masu daraja.
11Za mu yi ’yan kunnenki na zinariya, da adon azurfa.
12Yayinda sarki yake a teburinsa, turarena ya bazu da ƙanshi.
13Ƙaunataccena yana kamar ƙanshin mur a gare ni, kwance a tsakanin ƙirjina.
14Ƙaunataccena kamar tarin furanni jeji ne gare ni daga gonakin inabin En Gedi.
15Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata! Kai, ke kyakkyawa ce! Idanunki kamar na kurciya ne.
16Kai kyakkyawa ne, ƙaunataccena! Kai, kana ɗaukan hankali! Gadonmu koriyar ciyawa ce.
17Al’ul su ne ginshiƙan gidanmu; fir su ne katakan rufin gidanmu.
tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
WEBREATH · 11:11
«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath