Zabura 88
1Ya Ubangiji, Allah wanda ya cece ni, dare da rana ina kuka a gabanka.
2Bari addu’ata ta zo a gabanka; ka kasa kunne ga kukata.
3Gama raina yana cike da wahala rayuwata tana gab da kabari.
4An lissafta ni cikin waɗanda suka gangara zuwa cikin rami; ni kamar mutumin da ba shi da ƙarfi ne.
5An ware ni tare da matattu, kamar waɗanda aka kashe da suke kwance a kabari, waɗanda ba ka ƙara tunawa, waɗanda aka yanke daga taimakonka.
6Ka sa ni a ramin da yake can ƙasa cikin zurfafa mafi duhu.
7Hasalarka tana da nauyi a kaina; ka turmushe ni da dukan raƙumanka. Sela
8Ka ɗauke abokaina na kurkusa daga gare ni ka sa na zama abin ƙyama a gare su. An kange ni, ba yadda zan kuɓuta
9idanuna ba sa gani sosai saboda baƙin ciki. Ina kira gare ka, ya Ubangiji, kowace rana; na tā da hannuwana zuwa gare ka.
10Kakan nuna wa matattu ayyukanka na banmamaki ne? Waɗanda suka mutu sukan tashi su yabe ka ne? Sela
11Ana furta ƙaunar a cikin kabari ne, ana zancen amincinka a cikin Hallaka ne?
12An san ayyukanka masu banmamaki a wurin duhu ne, ko ayyukan adalcinka a lahira?
13Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji; da safe addu’ata kan zo gabanka.
14Don me, ya Ubangiji, ka ƙi ni ka kuma ɓoye fuskarka daga gare ni?
15Tun ina ƙarami na sha wahala na kuma yi kusa in mutu; na sha wahalar razanarka kuma na kuma fid da zuciya.
16Hasalarka ta sha kaina; razanarka ta hallaka ni.
17Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa; sun mamaye ni ɗungum.
18Ka ɗauke abokaina da ƙaunatattuna daga gare ni; duhu ne abokina na kurkusa.
tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
WEBREATH · 11:11
«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath