Zabura 85
1Ka nuna wa ƙasarka alheri, ya Ubangiji; ka mai da nasarorin Yaƙub.
2Ka gafarta laifin mutanenka ka kuma shafe dukan zunubansu. Sela
3Ka kau da dukan fushinka ka kuma juye daga hasalar fushinka.
4Ka sāke mai da mu, ya Allah Mai Cetonmu, ka kau da rashin jin daɗinka daga gare mu.
5Za ka ci gaba da fushi da mu har abada ne? Za ka ja fushinka cikin dukan tsararraki?
6Ba za ka sāke raya mu ba, don mutanenka su yi farin ciki a cikinka?
7Ka nuna mana ƙaunarka marar ƙarewa, ya Ubangiji, ka kuma ba mu cetonka.
8Zan saurari abin da Allah Ubangiji zai faɗa; ya yi alkawarin salama ga mutanensa, tsarkakansa, amma kada su koma ga wauta.
9Tabbatacce cetonsa yana kusa da waɗanda suke tsoronsa, don ɗaukakarsa ta zauna a cikin ƙasarmu.
10Ƙauna da aminci za su sadu; adalci da salama za su yi wa juna sumba.
11Aminci zai ɓulɓulo daga ƙasa, adalci kuma yă duba daga sama.
12Ubangiji tabbatacce zai bayar da abin da yake da kyau, ƙasarmu kuwa za tă ba da amfaninta.
13Adalci na tafiya a gabansa yana shirya hanya domin ƙafafunsa.
tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
WEBREATH · 11:11
«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath