Zabura 76
1A cikin Yahuda an san Allah; sunansa da girma yake a cikin Isra’ila.
2Tentinsa yana a Salem mazauninsa yana a Sihiyona.
3A can ya kakkarya kibiyoyin wuta, garkuwoyi da takuban, makaman yaƙi. Sela
4Darajarka tana da haske, fiye da darajar tuddai waɗanda suke cike da namun jeji masu yawa.
5Jarumawa sun zube kamar ganima sun yi barcinsu na ƙarshe; ba ko jarumi guda da zai iya ɗaga hannuwansa.
6A tsawatawarka, ya Allah na Yaƙub, doki da keken yaƙi suka kwanta ba motsi.
7Kai kaɗai ne za a ji tsoro. Wane ne zai iya tsayawa sa’ad da ka yi fushi?
8Daga sama ka yi shelar hukunci, ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit,
9sa’ad da kai, ya Allah, ka tashi don ka yi shari’a, don ka cece dukan masu shan wahala a ƙasar. Sela
10Tabbatacce fushinka a kan mutane kan jawo maka yabo, waɗanda suka tsira daga fushinka za su zama kamar rawaninka.
11Ku yi alkawari wa Ubangiji Allahnku ku kuma cika su; bari dukan ƙasashen maƙwabta su kawo kyautai ga Wannan da za a ji tsoro.
12Ya kakkarya ƙarfin masu mulki; sarakunan duniya suna tsoronsa.
tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
WEBREATH · 11:11
«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath