Kiristanci
baya

Zabura 75

1Muna maka godiya, ya Allah, muna maka godiya, gama Sunanka yana kusa; mutane na faɗin ayyukanka masu banmamaki.

2Ka ce, “Na zaɓi ƙayyadadden lokaci; ni ne wanda yake shari’ar gaskiya.

3Sa’ad da duniya da dukan mutanenta suka girgiza, ni ne wanda na riƙe ginshiƙan daram. Sela

4Ga masu girman kai na ce, ‘Kada ku ƙara taƙama,’ ga mugaye kuma, ‘Kada ku ɗaga ƙahoninku.

5Kada ku ɗaga ƙahoninku gāba da sama; kada ku yi magana da miƙaƙƙen wuya.’ ”

6Ba wani daga gabas ko yamma ko hamada da zai ɗaukaka mutum.

7Amma Allah ne mai yin shari’a, yakan saukar da wannan, yă kuma tayar da wani.

8A hannun Ubangiji akwai kwaf cike da ruwan inabi mai kumfa gauraye da kayan yaji; yakan zuba shi, dukan mugayen duniya kuwa su sha shi tas.

9Game da ni dai, zan furta wannan har abada; zan rera yabo ga Allah na Yaƙub,

10wanda ya ce, “Zan yanke ƙahonin dukan mugaye, amma za a ɗaga ƙahonin adalai sama.”

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath