Kiristanci
baya

Zabura 67

1Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, Sela

2don a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma a cikin dukan al’ummai.

3Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe ka.

4Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki, gama kana mulkin mutanenka da adalci kana kuma bi da al’umman duniya. Sela

5Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe.

6Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu.

7Allah yă sa mana albarka, dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath