Zabura 61
1Ka ji kukata, ya Allah; ka saurari addu’ata.
2Daga iyakar duniya na yi kira gare ka, na yi kira yayinda zuciyata ta karai; ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi.
3Gama kai ne mafakata, hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi.
4Ina marmari in zauna a tentinka har abada in sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka. Sela
5Gama ka ji alkawarina, ya Allah; ka ba ni gādo na waɗanda suke tsoron sunanka.
6Ka ƙara kwanakin ran sarki, shekarunsa su kasance a zamanai masu yawa.
7Bari yă yi mulki a gaban Allah har abada; ka sa ƙaunarka da amincinka su tsare shi.
8Sa’an nan zan riƙa rera yabo ga sunanka in kuma cika alkawarina kowace rana.
tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
WEBREATH · 11:11
«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath