Kiristanci
baya

Zabura 58

1Ku masu mulki tabbatacce kuna magana daidai? Kuna yin shari’a daidai a cikin mutane?

2Sam, a zuciyarku kuna ƙirƙiro rashin adalci, da hannuwanku kuma kuna tā da hargitsi a duniya.

3Kai, tun haihuwa mugaye sukan kauce; daga cikin ciki, su lalatattu ne maƙaryata.

4Dafinsu ya yi kamar dafin maciji, kamar na gamsheƙan da ya toshe kunnuwansa,

5da ba ya jin muryar gardi, kome dabarar gwanin mai waƙar zai zama.

6Ka kakkarya haƙoran a bakunansu, ya Allah; ka yayyage fiƙoƙin zakoki, ya Ubangiji!

7Bari su ɓace kamar ruwa mai wucewa; sa’ad da suka ja bakansu, bari kibiyoyinsu su murtsuke.

8Kamar katantanwun da suke narkewa yayinda suke tafiya, kamar jinjirin da aka haifa matacce, kada su ga hasken rana.

9Kafin tukwanenka su ji zafin ƙayayyuwa, ko su kore ne ko busasshe, za a shafe mugaye.

10Masu adalci za su yi murna sa’ad da aka rama musu, sa’ad da suka wanke ƙafafunsu cikin jinin mugaye.

11Sa’an nan mutane za su ce, “Tabbatacce har yanzu ana sāka wa adalai; tabbatacce akwai Allahn da yake shari’anta duniya.”

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath