Kiristanci
baya

Zabura 56

1Ka yi mini jinƙai, ya Allah, gama mutane sun tasar mini da zafi; dukan yini suna matsa harinsu.

2Masu ɓata sunana suna bina dukan yini; da yawa suna kai mini hari cikin fariyarsu.

3Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka.

4Ga Allah wanda maganarsa nake yabo ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba. Me mutum mai mutuwa zai yi mini?

5Dukan yini sun yi ta juya maganata; kullum suna ƙulle-ƙulle su cuce ni.

6Sun haɗa baki, sun ɓoye, suna kallon takawata suna a shirye su ɗauki raina.

7Sam, kada ka bari su kuɓuce; cikin fushinka, ya Allah, ka saukar da al’ummai.

8Ka lissafta makokina; ka jera hawayena a littafinka, ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?

9Ta haka abokan gābana za su juya da baya sa’ad da na nemi taimako. Ta haka zan san cewa Allah yana tare da ni.

10Ga Allah, wanda nake yabon maganarsa, ga Ubangiji, wanda nake yabon maganarsa,

11ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?

12Ina ƙarƙashin alkawari gare ka, ya Allah; zan miƙa hadayuna na godiya gare ka.

13Gama ka cece ni daga mutuwa da kuma ƙafafun daga tuntuɓe, don in yi tafiya a gaban Allah cikin hasken rai.

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath