Kiristanci
baya

Zabura 36

1Akwai magana a cikin zuciyata game da zunubin mugu. Babu tsoron Allah a idanunsa.

2Gama a idanunsa yana ganin kansa wani abu ne wanda ya sha ƙarfi a gane ko ya ƙi zunubinsa.

3Kalmomin bakinsa mugaye ne da kuma ruɗu; ya daina zama mai hikima da yin alheri.

4Ko a kan gadonsa ma yana shirya mugunta; yakan sa kansa ga aikata zunubi kuma ba ya ƙin abin da ba shi da kyau.

5Ƙaunarka, ya Ubangiji, kan kai sammai, amincinka har sararin sammai.

6Adalcinka yana kama da manyan duwatsu, hukuncinka kamar zurfi mai girma. Ya Ubangiji, kana lura da mutum da dabba.

7Ina misalin ƙaunarka marar ƙarewa! Mutane manya da ƙanana kan sami mafaka cikin inuwar fikafikanka.

8Suna biki a yalwar gidanka; kakan ba su sha daga rafin farin cikinka.

9Gama a gare ka akwai maɓulɓular rai cikin haskenka mukan ga haske.

10Ka ci gaba da ƙaunarka ga waɗanda suka san ka, adalcinka ga masu gaskiyar zuciya.

11Kada ka bari ƙafar mai girman kai yă fāɗa mini, ko hannun mugu ya kore ni.

12Dubi yadda masu aikata zunubi suka fāɗi, a zube, ba za su kuwa iya tashi ba!

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath